Jami’an Hisbah Sun Kama Mata Masu Yawan Gaske Saboda Kwankwadar Barasa Da Karuwanci A Wata Jihar Arewa
- Hukumar Hisbah reshen Jigawa tace ta kama mutum 31 kan aikata munanan dabi’u a jihar
- Yan Hisbah sun cika hannu da mata da yawa kan zargin aikata masha’a da kuma kwankwadar barasa
- Kwamandan hukumar, Ibrahim Dahiru ya sha alwashin yakar duk wasu munanan dabi’u a yankunan jihar
Jigawa - Jami'an hukumar hisbah, sun kama mutum 31 a jihar Jigawa saboda aikata rashin da'a.
Kwamandan hukumar Hisbah a jihar, Ibrahim Dahiru, ya bayyana a ranar Laraba, cewa an kama masu laifin ne da misalin karfe 6:00 na safe kan zargin aikata karuwanci da kuma kwankwadar barasa.
Ya ce wadanda ake zargin sun hada da mata 25 a karamar hukumar Kazaure da ke jihar, jaridar The Cable ta rahoto.
Dahiru yace an kama mutanen ne yayin wani samame na hukumar Hisbah mai taken "ka girbe abun da ka shuka."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kwamandan yace an kwashe kwalaben barasa iri-iri guda 55 da lita 50 na burkutu.
Ya ce an mika masu laifin da abubuwan da aka kwato zuwa hannun yan sanda a yankin don daukar mataki.
Dahiru ya jinjinawa mazauna jihar kan goyon baya da hadin kai da suke ba hukumar.
Ya ba jama'a tabbacin cewa Hisbah zata ci gaba da yaki da munanan dabi'u a fadin jihar, rahoton Sahara Reporters.
Duk da kokarin Hisbah na hana shan barasa, 'yan Najeriya sun kwankwadi ta N600bn a wata shida
A wani labarin kuma, wani rahoton da kafar yada labarai ta BBC ta fitar ya ce, akalla barasar N599.11 ne 'yan Najeriya suka kwankwada a cikin watanni shida kacal na farkon 2022.
Rahoton ya fito ne daga kamfanonin barasa hudu na Najeriya, kuma ya mai da hankali ne daga watan Janairun bana zuwa watan Yunin da ta gabata.
Guinness da Champion na daga cikin kamfanonin hudu, kuma sun ce kwalliya ta biya kudin sabulu, domin kuwa kamfanonin barasa a Najeriya sun samu riba mai tsoka a wannan shekarar.
Asali: Legit.ng