Kallon Mamakin da Buhari Yayi wa Shigar Ezra Olubi a Wurin Bada Lambar Yabo ya Janyo Cece-kuce
- Jama’a sun cika da mamaki bayan bayyanar wani bidiyo na shugaban kamfanin Paystack, Ezra Olubi da shugaban kasa Muhammadu Buhari
- A cikin bidiyon, an gano Olubi cikin shiga ta bakaken kaya yayin da ya amshi lambar yabonsa daga wajen shugaban kasar
- Sai dai kuma, yanayin kallon da shugaban Najeriyan ya yiwa shigar Olubi wanda ya goga bakin jan-baki ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba yan Najeriya da dama lambar yabo a ranar Talata, 11 ga watan Oktoban 2022.
Daga cikin wadanda suka amshi lambar yabo harda Ezra Olubi, shugaban kamfanin Paystack, wani dandalin biyan kudi na kasa da kasa.
Sai dai kuma, alamu sun nuna Buhari bai yi tsammanin ganin Olubi cikin yanayin shigar da bayyana ba.
Wani bidiyo da ke nuna lokacin da Olubi ya karbi lambar girmamawarsa ya yadu a shafukan soshiyal midiya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cikin bidiyon, an gano Buhari ya saki baki yana kallon yanayin shigar Olubi wanda ciki harda bakin jan-baki ya goga a labbansa.
Kalli wallafar a kasa:
Mabiya shafukan soshiyal midiya sun yi martani ga bidiyon Buhari/Olubi
mc_ichie:
“Abun da ya dace da Buhari kenan..Dama siketi da riga gayen ya saka.”
lucci_okoye:
“Yayin da baka ma san mutanen da kake sanyawa a lissafinka ba amma dai kudin da kamfanin ke kawowa ne kawai ke shiga idonka.”
kv_by_kelvin_:
"Lmaoooooooo. A ture batun wasa akwai shigar da ake yiwa kowani irin taro. Kuma wannan shigar ba ta irin wannan taron bane. Idan zaka je shakatawa da abokai, eh amma zuwa ganin shugaban jasa ((duk da cewar ban damu da wannan ba) ba daidai bane. Ka yi shiga ta kamala.!”
mz_barbss:
“Ina ganin jan-bakin ne saboda kayan bai yi muni sosai ba..”
Tsohon Gwamnan Da Buhari Ya Yi Wa Afuwa Ya Fadi Yadda Za'a Kawo Karshen Cin Hanci da Rashawa a Najeriya
A wani labarin, tsohon gwaman jihar Plateau, Joshua Dariye, ya bayyana cewa za a iya kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar nan idan har kowani dan Najeriya zai bayar da hadin kai.
Sanatan ya bayyana hakan ne a a ranar Litinin, yayin wata hira da gidan talbijin din Channels a shirin NewsNight.
Dariye ya kuma bayyana cewa hukunta shi da aka yi tare da tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame, kan aikata rashawa bai kawo karshen sama da fadi da ake yi kan dukiyar kasar ba.
Asali: Legit.ng