Mutane 447 Daga 5,000 Suka Samu Lambar Karramawa Ta Kasa, Ministan Buhari

Mutane 447 Daga 5,000 Suka Samu Lambar Karramawa Ta Kasa, Ministan Buhari

  • Ministan ayyuka na musamman, George Akume, yace mutum 447 ne suka samu lambar karrama wa ta ƙasa daga cikin 5000
  • Akume ya yi bayanin cewa mutanen da suka kunshi yan Najeriya da kawayen Najeriya sun ba da gudummuwa a fannoni daban-daban
  • Manyan ƙusoshin gwamnatin tarayya sun halarci taron wanda ya gudana a ICC dake Abuja yau Talata

Abuja - Jumullar mutane 447 daga cikin mutum 5,000 da aka zaƙulo ne suka samu karrama wa ta ƙasa inji ministan ayyuka na musamman, George Akume, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Akume ya bayyana haka ne yayin da yake jawabin maraba a wurin bikin karramawa da aka shirya a babban ɗakin taro na kasa da ƙasa (ICC) dake Abuja ranar Talata.

Kara karanta wannan

Jinkirin Karasa Layin Dogon Kaduna Zuwa Kano: Gwamnatin China Ta Hana Najeriya Bashi

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Mutane 447 Daga 5,000 Suka Samu Lambar Karramawa Ta Kasa, Ministan Buhari Hoto: vanguard
Asali: UGC

A cewar ministan, mutane 447 ne kacal suka tsallake suka shiga jerin waɗanda za'a karrama daga cikin waɗanda aka zaɓo daga sassa daban-daban na gwamnati da masu zaman kansu.

Karramawa ta ƙasa ta ginu ne daga dokar girmamawa ta ƙasa mai lamba 6 a 1964, kuma ta fara ne tun kafin wannan lokacin a ranar 1 ga watan Oktoba, 1963.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dokar ta baiwa shugaban ƙasa cikakken ikon karrama yan ƙasa da suka cancanta, waɗanda suka ba da gudummuwa wajen cigaban ƙasa ta kowane fannin rayuwa.

A bayanin Ministan, mazauna da yan kasashen waje 447 da aka yi wa laƙabi da, "Yan Najeriya da ƙawayen Najeriya," suka sami lambar karramawa daga Grand Commander of the Order of the Niger (GCON) zuwa lambar yabon tarayya.

Waɗanda aka karrama da GCON sun haɗa da tsohuwar ministar kuɗi, Ngozi Okonjo-Iweala; shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, Alƙalin alƙalai na yanzu, Olukayode Ariwoola da tsohon Alkalin Alkalai, Tanko Muhammed.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Mummunan Hari, Sun Kashe Mai Anguwa da Wasu Mutune a Jihar Arewa

Sauran sune, mataimakiyar shugaban majalisar ɗinkin duniya, Amina Muhammed, da kuma tsohon shugaban taron majalisar ɗinkin duniya, Tijjani Mohammed-Bande.

Haka zalika, daga cikin mutum 13 da aka girmama bayan rasuwarsu akwai tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, Abba Kyari, tsohon hafsan sojin ƙasa, Janar Ibrahim Attahiru, matuƙin jirgin soji, Matthew Oyedepo.

Manyan mutanen da suka halarci taron

Manyan mutanen da suka ƙara wa taron armashi sun haɗa da mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Sai kuma Alƙalin Alƙalai, Olukayode Ariwoola, shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, Hafsoshin tsaro da Sufetan yan sanda na ƙasa, Usaman Baba.

Bugu da ƙari, ba'a bar Sarakuna a baya ba wajen halartar taron kuma daga cikinsu akwai Sarkin Lafia, Sidi Muhammed, wanda shi ne shugaban kwamitin ba da lambar yabo na ƙasa.

A wani labarin kuma kun ji cewa Shugaba Buhari Ya Karrama Buratai Da Babban Lambar Yabo Na Kasa

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe $100m wajen ciyar da daliban makaranta 10m

An fitar da cikakken jerin sunayen wadanda za a bawa lambar yabo na kasa a Najeriya inda suka dara 400.

Tsohon babban hafsan sojojin kasan Najeriya kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin T.Y Buratai na cikin wadanda za a karrama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262