'Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Karamar Hukuma a Jihar Ebonyi

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Karamar Hukuma a Jihar Ebonyi

  • Miyagun 'yan bindiga sun bi dare, sun cinna wa wani sashin ƙaramar hukumar Ezza ta arewa a jihar Ebonyi, kudu maso gabashin Najeriya
  • Shugaban ƙaramar hukumar, Chief Ogodo Ali Nomeh, ya ce maharan sun lalata muhimman abubuwa da suka kai darajar miliyoyin Naira
  • Yan sanda sun yi kokarin fatattakarsu, a halin yanzun jami'an tsaro sun bazama da nufin cafke maharan baki ɗaya

Ebonyi - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun ƙone sashin hedkwatar ƙaramar hukumar Ezza ta arewa a jihar Ebonyi, sun lalata muhimman kayayyaki da takardu na miliyoyin naira.

Shugaban ƙaramar hukumar, Chief Ogodo Ali Nomeh, shi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a Abakaliki ranar Litinin, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Ofishin Yan Sanda, Sun Tafka Mummunar Ɓarna

Matsalar tsaro a Kudu maso gabas.
'Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Karamar Hukuma a Jihar Ebonyi Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Chief Nomeh yace tsageru kusan 20 suka kutsa yankin da misalin ƙarfe 1:30 na dare, suka tafi kai tsaye suka babbaka dakin ajiya na ƙaramar hukuma.

Yace dakarun 'yan sanda sun yi nasarar dakile shirin masu ta da gobarar, kuma sakamakon haka da yawan maharan sun gudu da raunukan harsashin bindiga a jikinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wutar ta yi kaca-kaca da sabbin masuburbudar sanyi (AC) da aka siyo domin gyara Sakateriyar, wasu takardu, injina da kuma kayayyakin Ofisoshi," inji shi.

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Shugaban ƙaramar hukumar ya ƙara da cewa 'yan Bangan yankin da dakarun hukumomin tsaro sun bazama kurfa-kurfa domin damko maharan, waɗanda ake kyautata zaton sun raunata.

Bugu da ƙari, Mista Nomeh, ya nuna kwarin guiwarsa cewa nan ba da jima wa ba zasu shiga hannu kuma su amsa laifukansu domin su girbi abin da suka shuka, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Fitaccen Dan Siyasa Kuma Na Kusa da Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Rasu

A wani labarin na daban kuma Wasu Miyagun Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Basarake A Arewacin Najeriya

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da hakimin kauyen Iyaka da ke masarautar Gummi a jihar Zamfara.

Maharan sun farmaki kauyen ne da misalin karfe 1:45 na ranar Lahadi, 9 ga watan Oktoba bayan sun ajiye baburansu a jeji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel