Gwamna Jigawa Ya Sha Ihu a Wurin Bikin Murnar Haihuwar Annabi SAW
- Gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar, ya halarci bikin al'ada da aka saba shiryawa duk shekara a Masarautar Gumel lokacin Maulidi
- Sai dai mutane da basu ji dadin halin da gwamnan ya nuna game da Ambaliyar ruwa ba sun masa ihun 'Bamayi Bamayi'
- Mai magana yawun gwamnan Jigawa, Habibu Kila, ya musanta faruwar lamarin yayin da aka tuntube shi
Jigawa - Mutane sun yi wa Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, da mataimakinsa, Umar Namadi, ihun rashin gamsuwa a ƙaramar hukumar Gumel ranar Asabar da ta gabata.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Gwamna Badaru ya ziyarci Gumel ne domin halartar Maulidi, watau bikin murnar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammd (SAW).
Tun farko dai kwamishinan ayyuka na musamman a Jigawa, Auwal Sankara, ya sanar da cewa Mai gidansa zai halarci shagalin "Sallah Gani" da ake shiryawa duk shekara.
"Mai girma gwamnan Jigawa, Alhaji Muhammed Badaru Abubakar, tare da Sarkin Gumel, zai gudanar da bikin Sallah Gani wanda aka shirya ranar Asabar a Masarautar Gumel."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Sallah Gani, wata dadaddiyar al'ada ce da ake gudanarwa a Masarautar Gumel duk shekara a watan Maulidi, musamman ranar 12 ga watan Rabiul Awwal na Kalandar Musulunci."
"Ya'ya maza da mata 'yan asalin yankin masarautar Gumel daga ko ina rayuwa ta kaisu, sukan koma gida domin halartar bikin Al'adar mai matuƙar muhimmanci."
- Auwal Sankara.
Meyasa mutane suka musu Ihu?
Legit.ng Hausa ta gano cewa zuwan Badaru wurin bikin shi ne karo na farko da gwamnan ya halarci wani taro a fili tun bayan dawowarsa daga ƙasar waje inda ya tafi hutawa.
Gwamna Badaru ya sha matsin lamba da suka bisa wanke ƙafa ya tafi hutu ba tare da jimami da ziyartar mutanen da ibtila'in Ambaliyar ruwa ta shafa a jihar ba.
Sama da mutum 100 aka tabbatar sun mutu sakamakon Ambaliyar, wacce ta lalata gonakin mutane da gidaje kuma ta raba dubbanni da mahallansu.
A wurin taron a garin Gumel, wani bidiyo ya nuna yadda mutane suka rinka ɗaga murya suna wa gwamnan da mataimakinsa ihun bamayi.
Mazauna garin sun ci gaba da faɗin 'Bamayi' yayin da gwamnan da mataimakinsa ke daga musu hannu daga cikin motarsu dake tafiya.
Haka zalika, da yawan mutane sun girmama tare da gaida gwamnan lokacin da yake wuce wa zuwa fadar Sarki, inda taron ke gudana.
Duk da babu tabbacin dalilin yi wa gwamnan Ihun bamayi, mutane na ganin hakan ta faru ne sakamakon nuna halin ko in kula ga jama'ar da ambaliyar ruwa ta taba a Jigawa.
Yayin da aka tuntube shi ranar Lahadi, kakakin gwamnan, Habibu Kila, yace, "Ba gaskiya bane."
A wani labarin kuma kun ji cewa wani Mummunan Hatsarin Mota Ya Faru A Jigawa, An Rasa Rayyuka
Mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin mota da ya ta faru a Jihar Jigawa.
Mai magana da yawun rundunar tsaro ta NSCDC na Jihar Jigawa, Adamu Shehu ya tabbatar da afkuwar hatsarin.
Asali: Legit.ng