Zargin Sakin ‘Yan Boko Haram 101 daga Magarkamar Kirikiri Ya Tada Hankula

Zargin Sakin ‘Yan Boko Haram 101 daga Magarkamar Kirikiri Ya Tada Hankula

  • Ana zargin gwamnatin tarayya da sakin wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne har su 101 daga magarkamar Kirikiri dake jihar Legas
  • Sai dai daya daga cikin mazauna gidan gyaran halin ya tabbatar da cewa ‘yan Boko Haram 101 an sake su ne don karbo sauran fasinjoji 23 na harin jirgin kasa
  • Wani jami’in gidan yarin ya musanta faruwar hakan amma yace a yanzu ana wata shari’a ta sakin wadanda ake zargi da ta’addanci aka garkamesu tun 2009

Legas - A kalla mutum 101 da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne ake zargin an saki daga gidan yarin Kirikiri dake jihar Legas, jaridar Punch ta rahoto hakan.

Kamar yadda shafin yanar gizo na gidauniyar jaridancin bincike ya bayyana, ma’aikatan gidan yarin sun bude musu hanya tare da sakinsu suka kama gabansu duk daga cikin yarjejeniyar sakin sauran fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wadanda aka sace a ranar 28 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Mata da Yara 30 Sun Yi Shahada, Sun Nutse a Ruwa Za Su Tserewa ‘Yan Bindiga

Majiyar tace wadanda aka sakin duk suna jiran a kammala shari’arsu ne wacce aka fara a 2009 kuma dukkansu sun san batun balle magarkamar Kuje da ‘yan ta’adda suka yi tun kafin lamarin ya faru.

“A sirrance suka saki mutum 101 da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne wurin karfe 6 na safe. An kwashe watanni ana yarjejeniyar. Tare muke sallah da su kuma a yayin da muke wurin sallah ne suka sanar da ni cewa zasu tafi gida a watan Oktoba.
“Tun safiyar Asabar, an bude kofar inda suke garkame kuma aka kira su. Sun mayar da kayansu tuni. Na saba magana da wani Adamu a daki na G3 amma a yanzu baya nan. Dogo ne, siriri kuma yana da doguwar fuska.
“Sun sanar min cewa za a sake su ne biyo bayan wata yarjejeniya da kuma yadda wadanda ke daukar nauyinsu suka matsawa Buhari lamba. Suna tunanin idan ba a sake su ba har aka yin sabon shugaban kasa wanda ba ‘dan kabilarsu bane, ba zasu samu rangwame ba.”

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito: 'Yadda Muka Shawo Kan Yan Ta'adda Suka Sako Ragowar Fasinjojin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja'

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Majiyar tace.

Sai dai wani jami’i a gidan yarin ya musanta wannan ikirarin.

Majiyar tace ana ta kokarin sakin wadanda ake zargin ne saboda yadda aka tsare su ba bisa ka’ida ba.

“Akwai shari’ar da ake yi na kan yadda za a saki wasu da aka garkame saboda an ajiyesu tun a shekarar 2009 ba tare da an yi shari’arsu ba. Har yanzu ba a kammala ba kamar yadda na sani balle a saki wasu.”

- Jami’in ya kara da cewa.

An yi kokarin zantawa da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali kan lamarin amma har yanzu ba a samu dama ba.

Bidiyon Turnukun Yaki Tsakanin Boko Haram da ISWAP, ‘Yan Boko Haram 8 Sun Sheka Lahira

A wani labari na daban, mayakan ta’addanci na ISWAP sun halaka mayaka takwas na kungiyar ta’addancin Boko Haram a wata arangama da suka yi a Borno.

Kara karanta wannan

Yadda Hadimin Gumi ya Dinga Tarwatsa Kokarin FG na Ceto Fasinjojin Jirgin Kasa, Jami’i

ISWAP tsagi ne ba kungiyar ta’addancin Boko Haram kuma sun rabe ne sakamakon rikicin shugabanci.

Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana, kungiyoyin ta’addancin biyu sun yi arangama ne a ranar Alhamis wurin Krinowa dake Marte.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng