Yan Bindiga Sun Babbake Ofishin Yan Sanda, Jami'i Sun Rasa Rayukansu a Enugu

Yan Bindiga Sun Babbake Ofishin Yan Sanda, Jami'i Sun Rasa Rayukansu a Enugu

  • Yan bindiga sun kai hari Ofishin yan sandan dake yankin Arum Inyi, ƙaramar hukumar Oji-River a jihar Enugu
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun kashe 'yan sanda biyu a bakin aiki, sun kwashi makamai sun ƙona Caji Ofis ɗin
  • Hukumar yan sanda reshen jihar Enugu ba tace komai ba kan sabon harin wanda ya faru da safiyar Lahadin nan

Enugu - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai farmaki Caji Ofis ɗin Inyi ɗake ƙaramar hukumar Oji-River, jihar Enugu, inda suka kashe 'yan sanda biyu a bakin aiki.

Maharan sun kuma cinna wa Ofishin wuta bayan tattara bindigu da Alburusai suka yi gaba da su a harin, wanda ya auku da safiyar ranar Lahadi a Ofishin yan sanda da ke Arum Inyi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Mummunan Hari, Sun Kashe Mai Anguwa da Wasu Mutune a Jihar Arewa

Caji Ofis a jihar Enugu.
Yan Bindiga Sun Babbake Ofishin Yan Sanda, Jami'i Sun Rasa Rayukansu a Enugu Hoto: SaharaReporters
Asali: Twitter

A wani bidiyo da wakilin jaridar Punch ya ci karo da shi ya nuna gawar mutum biyu da ake tsammanin 'yan sanda ne kwance a gaban harabar Ofishin.

Bidiyon ya nuna yadda Rufin Caji Ofis ɗin ke ci da wuta. Kazalika muryar dake magana a Bidiyon ta ayyana ɗaya daga cikin gawarwakin a matsayin ɗan sanda amma babu tabbaci game da ɗayan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin garin Arum Inyi, wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa:

"A zahirin gaskiyar ranar Asabar na bar ƙauyen zuwa Enugu amma na samu labari daga mutanen mu cewa 'yan bindiga sun kai hari Caji Ofis ɗin ƙauyen mu, sun kashe ɗan sanda ɗaya, a yanzu banda cikakken bayani."

An gargaɗi mutane su kula

Legit.ng Hausa ta gano cewa wani sakon tsaro da ake yaɗa wa a kafafen sada zumunta a babban birnin jihar Enugu, ya gargaɗi mutanen yankin da kewaye su kula sosai da motsinsu saboda tsaro.

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Ko Kwankwaso? An Bayyana Dan Takarar Da Ya Shirya Ceto Najeriya Idan Ya Gaji Buhari a 2023

Duk wani yunkurin jin ta bakin hukumar yan sandan Enugu ya ci tura domin mai magana da yawun hukumar, DSP Daniel Ndukwe, ba ya ɗaga kira ko amsa sakonni, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Gunduma da Wasu Mutum Uku a Jihar Filato

'Yan bindiga sun kashe Mai Anguwa da wasu mutum uku a wani sabon hari da suka kai yankin ƙaramar hukumar Bokkos a Filato.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun shiga ƙauyen Kulias (Mabel) suka buɗe wa mutane wuta kan mai uwa da wabi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262