Hankula Sun Tashi Yayin Da Aka Nemi Mutum 30 Aka Rasa Sakamakon Kifewar Kwale-Kwale A Wata Jihar Najeriya

Hankula Sun Tashi Yayin Da Aka Nemi Mutum 30 Aka Rasa Sakamakon Kifewar Kwale-Kwale A Wata Jihar Najeriya

  • Mutanen garin Umunnankwo a karamar hukumar Ogbaru suna cikin alhini bisa rasuwar ƴaƴansu maza da mata a hatsarin jirgin ruwa
  • Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ruwan ya taso ne daga gadan Onukwu zai nufi kasuwar Nkwo da Ogbakuba a karamar hukumar ta Ogbaru
  • Baya ga wadanda suka rasu cikin fasinjojin kimanin 50 da ke cikin jirgin, har yanzu ana neman wasu mutane 30 ba a gansu ba

Jihar Anambra - A kalla mutane 30 ne aka ce sun ɓace a yayin da kwale-kwale da ke dauke da mutane 50 ya kife a garin Umunnankwo da ke karamar hukumar Ogbaru na jihar Anambra.

Abin bakin cikin ya faru ne a ranar Juma'a 7 ga watan Oktoba, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

'A Soke EFCC,' Matasan Ibadan Suka Fada Wa FG, Sun Yi Babban Zanga-Zanga

Jirgin ruwa
Hankula Sun Tashi Yayin Da Aka Nemi Mutum 30 Aka Rasa Sakamakon Kifewar Kwale-Kwale A Wata Jihar Najeriya. Hoto: Nairaland
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar wadanda abin ya faru a idonsu, jirgin ruwan ya tashi daga gadan Onukwu ne ya nufi kasuwar Nkwo da Ogbakuba; duk a karamar hukumar Ogbaru, lokacin da ya kife.

Shaidan gani da idon ya ce kawo yanzu an nemi mutum 30 ba a gano su ba bayan faruwar lamarin.

Martanin shugaban karamar hukuma

Da ya ke tsokaci kan lamarin, shugaban kwamitin mika mulki na karamar hukumar Ogbaru, Pascal Aniegbuna, ya ce an ceto wasu fasinjojin wasu kuma sun rasu.

A bangarensa, dan majalisar tarayya mai wakiltar Ogbaru, Hon Victor Afam Ogene, ya nuna bakin cikinsa bisa hatsarin.

Ogene, wanda shine ɗan takarar majalisar tarayyar mai wakiltar mai wakiltar Ogbaru karkashin jam'iyyar Labour Party, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar ya ce ya girgiza bisa samun labarin hatsarin jirgin ruwan da ya yi sanadin rasuwar ƴaƴan garin maza da mata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Tsaron Ministan Abuja Hari

Ya ce:

"Mummunan labarin wannan hatsarin ya min ciwo matuka kuma na san ya girgiza mutane musamman yan uwan wadanda abin ya shafa. Wannan babban rashi ne ga garin Ogbaru baki daya.
"Ina mika ta'aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa da kuma mutanen Ogbahu, wanda a baya-bayan nan ambaliyar ruwa ya afka musu inda kusan garin baki daya ya nutse dubban mutane suka rasa muhalli."

Jinjiri Dan Wata 7 Da Mata 4 Sun Mutu A Hatsarin Kwale-Kwale A Jigawa

Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Jigawa ta tabbatar da rasuwar jinjiri dan wata bakwai da mata hudu a hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Guri.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar, DSP Lawan Shiisu, ne ya tabbatar da afkuwar lamarin a Dutse, ranar Laraba, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164