Biliyoyin da Shugabanni Suka Wawure Daga Najeriya Suna Dankare a Turai, Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koka kan kudaden kasar nan da aka wawushe kan yadda suke dankare a Turai
- Buhari ya ce abinda ke cin tuwo a kawarta shine yadda kasashen ketaren ke katantanewa tare da makale kudaden duk da na Najeriya
- Yace babban abin tunani a halin yanzu shine yadda rashawa tayi katutu a kasashen Afrika ta yadda ko an dawo da kudaden ba dole a amfana ba
Gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a guiwa ba har sai ta samo $5 biliyan da marigayi Janar Sani Abacha da iyalansa suka sace daga Najeriya tare da dankarawa a kasashen ketare kamar yadda shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace.
Shugaban kasan a wata wallafar ra’ayi da yayi a Financial Times ta London, ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun matukar jin dadin labarin kayan tarihi 72 wadanda aka fi sani da tagullar Benin da ake rike da su a gidan tarihi na Landan da sojojin Turai suka sace kan cewa za a dawo dasu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta rahoto cewa, kamar yadda yace, bukatar dawo da albarkatun da aka sace a yanzu ya zama dole.
“Biliyoyin da aka kwashe daga nahiyar nan ta hannun shugabanni suna nan dankare a asusun bankunan kasashen Turawa. Duk da Najeriya tana daya daga cikin kasashen da suka yi zarra a nahiyar Afrika wurin samo kudaden da aka sace, an samo kadan ne daga cikin kudaden.
“A farkon wannan shekarar, dole ta sa Najeriya ta dauka matakin shari’a kan Hukumar Kula da Laifuka ta Ingila saboda jinkirin dawo da kudaden da Abacha ya kwashe.”
- Buhari.
Sai dai yace, lamarin dake gaban kotun ya fallasa irin kalubalen dake gaban Najeriya.
Kamar yadda yace, idan aka duba matakin da rashawa ta kai a Afrika, abun dubawan shine ko za a yi amfani da kudaden da aka dawo da su yadda ya dace.
Buhari zai Gabatar da Kasafin Kudi a Yau, Tsaro ya Tsananta a Farfajiyar Majalisa
A wani labari na daban, an tsananta tsaro a majalisar tarayyan Najeriya kafin zuwan shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin gabatar da kasafin kudin 2023 a yau Juma’a.
Shugaban Kasan zai gabatar da kasafin N19.76 tiriliyan ga zauren gamayya na majalisar dattawa da wakilai da karfe 10 na safe.
Wannan ne karo na karshe da shugaban kasan zai gabatar da kasafin kudi gaban majalisar saboda wa’adin mulkinsa zai kare a watan Mayun 2023, Daily Trust ta rahoto hakan.
Asali: Legit.ng