Kiristocin CAN Ta Yaba Wa Buhari Bisa Ceto Fasinjojin Jirgin Kasa Abuja Zuwa Kaduna
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha yabo daga kungiyar CAN bisa ceto fasinjojin jirgin kasan Kaduna
- Kungiyar ta kuma yabawa wata kirista da ta dage da bin addininta duk da azabar da ta sha a hannun 'yan ta'adda
- An sace fasinjojin jirgin kasa sama da 50 a wani kazamin hari da 'yan ta'adda suka kai kan wani jirgin kasan da ya taso daga Abuja
Abuja - Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kokari wajen ganin an ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da aka sace a watannin baya.
Wasu tsageru sun yi awon gaba da fasinjojin jirgin kasan da ya taso daga Abuja zai wuce Kaduna a watan Maris, lamarin da ya tada hankalin 'yan Najeria.
Bayan sako wasu rukuni na fasinjojin da lokuta mabambanta, gwamnati ta samu nasarar karbo sauran mutum 23 da ke tsare a hannun tsagerun a yau Alhamis 6 ga watan Okotoba.
Buhari ya yi kokari
A nata martanin bayan samun labarin sako fasinjojin, kungiyar ta CAN ta ce tabbas shugaban ya yi kokari matuka wajen tabbatar an ceto jama'a a hannun 'yan ta'adda.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakazalika, kungiyar ta kuma yabawa wata fasinja, Lois Azurfa da ta dage kan riko da addininta na kirista, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Kungiyar ta ce Lois ta yi matukar kokari tunda bata bar kiristanci ba duk da rayuwa da ta yi a karkashin azabtarwar 'yan ta'addan da ake zargin 'yan Boko Haram ne.
BBC Hausa ta naqalto cewa, da yake karin haske, shugaban CAN na Najeriya, Aci-bishof Daniel Okoh yi tsokaci game da matashiyar mai shekaru 21, inda yace:
"Labarin matashiyar wata shaida ce cewa Ubangiji Mai girma yana tare da bayinsa, kuma zai kawo musu dauki ko da a bakin kura suke."
Daga karshe ya yabawa muhimmin kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi wajen tabbatar da wanzar da zaman lafiya da dakile matsalar tsaro a kasar.
'Yan IPOB Ba ’Yan Ta’adda Bane, Na Zauna da Su, Inji Peter Obi a 2017
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya taba kakabawa gwamnatin Najeriya laifi wajen ta'azzarar ayyukan barna daga 'yan awaren IPOB.
Ya kuma ga laifin gwamnati da ta ayyana kungiyar ta su Nnamdi Kanu a matsayin ta 'yan ta'adda, Premium Times ta ruwaito.
A ranar 1 ga watan Oktoban 2017 ne Peter Obi ya bayyana a gidan talabijin na Channels ya bayyana wadannan maganganu na ganin laifin gwamnati.
Asali: Legit.ng