Budurwa Yar Shekara 18 Ta Mutu A Hotel Daga Zuwan Wurin Shagalin Birthday

Budurwa Yar Shekara 18 Ta Mutu A Hotel Daga Zuwan Wurin Shagalin Birthday

  • Wata budurwa yar shekara 18 a duniya ta rasa rayuwarta daga zuwa wurin shagalin ƙarin shekara a jihar Oyo
  • Bayanai sun nuna cewa matashiyar mai suna Eniola ta bar gida tare da abokanta da nufin zuwa wurin Bazday amma sai gawarta
  • Hukumar yan sanda reshen jihar Oyo tace a halin yanzun jami'ai na kan bincike duk abinda aka gano zasu sanar da al'umma

Oyo - Wata budurwa yar shekara 18 a duniya mai suna Eniola ta rasa rayuwarta a wani Otal da ba'a bayyana sunansa ba da ke Titin Iwo, ƙaramar hukumar Ibadan ta arewa maso gabas a jihar Oyo.

Ganau sun shaida wa jaridar Vanguard cewa budurwar tare da wasu kawayenta da har yanzun ba'a tattara bayanansu ba sun je Otal ɗin ne domin halartar shagalin ƙarin shekara.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Bayan Shafe Watanni Uku, Yan Bindiga SUn Saki DPOn Yan Sandan Da Suka Sace

Taswirar jihar Oyo.
Budurwa Yar Shekara 18 Ta Mutu A Hotel Daga Zuwan Wurin Shagalin Birthday Hoto: vanguard
Asali: UGC

A cewar wata dattijuwa mai riƙe da ita, budurwar ta bar gida ranar Asabar da daddare tare da kawayenta da nufin zuwa wurin bikin ƙarin shekara.

Tsohuwar matar, wacce ta shiga cikin masu zanga-zanga a ƙofar Otal ɗin amma aka hana su shiga a wani Bidiyo da ake yaɗa wa, ta koka da cewa, "Nan ne Otal ɗin da suka zo shagalin."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yarinyar marainiya ce ta rasa iyayenta, ni nake ɗaukar ɗawainiyarta na yau da kullum, ban taba tunanin rayuwarta zata zo ƙarshe tun a shekarun ƙuruciya ba."
"Ya kamata shugaban Hotel ɗin nan ya hito da jerin waɗanda suka zauna da Adiresoshinsu, wannan zai taimaka wajen bin diddigin waɗanda suka aikata ɗanyen aikin."
"Na gaza yarda cewa ɗiyata ta mutu, ya zama tilas a zakulo wanda ya aikata ko ina ya shiga domin doka ta yi aiki a kansa."

Kara karanta wannan

Obi Ɗan-Gata: Gwamnoni 18 Ne Ke Marawa Obi Baya, Ohanaeze

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun 'yan sanda reshen jihar Oyo, Adewale Osifeso, yace a halin yanzu suna kan bincike ne amma zasu sanar da ci gaban da aka samu a lokacin da ya dace.

A wani labarin kuma kun ji cewa 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Jagoran Al'umma a Jihar Arewa

Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Sanannen jagoran al'umma, Gashon Leks, a yankin ƙaramar hukumar Mangu, jihar Filato.

Mazauna ƙauyen Daika, inda lamarin ya faru sun nuna damuwarsu saboda mutumin yana fama da rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262