Kungiyar ASUU Ta Maka Gwamnatin Tarayya a Kotu Saboda Yiwa Kishiyoyinta Rajista

Kungiyar ASUU Ta Maka Gwamnatin Tarayya a Kotu Saboda Yiwa Kishiyoyinta Rajista

  • Kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU ta maka gwamnatin Najeriya a kotu saboda yiwa CONUA da NAMDA rajista
  • ASUU ta shafe sama da watanni 7 tana yajin aiki saboda gwamnati ta gaza biya mata bukatun da ta gabatar
  • Hankalin gwamnatin Najeriya na kara karkata kan zaben 2023 mai zuwa, lamarin da ke kara bukatar shiri mai karfi

Abuja - Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) za ta tunkari kotun ma'aikata kan lamarin da gwamnati ta gabatar na yiwa kungiyoyin dake kishiyantarta rajista.

Lauyan ASUU, Femi Falana ne ya shaidawa Channels Tv cewa, kungiyar za ta tunkari kotun ma'aikata domin kai kokenta.

Hakazalika, shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi a ranar Alhamis 6 ga watan Okotoba.

ASUU ta kai karar Buhari kotu saboda yi mata kishiya
Kungiyar ASUU Ta Maka Gwamnatin Tarayya a Kotu Saboda Yiwa Kishiyoyinta Rajista | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar shugaban ASUU:

Kara karanta wannan

Tuna baya: Akwai kalaman da Peter Obi ya yi a baya dake nuna yana goyon bayan IPOB

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Shi (Falana) lauyanmu ne. Don haka, abin da ya fadi gaskiya ne."

Buhari ya yiwa ASUU kishiya

A ranar Talata ne gwamnatin Buhari ta amince da yiwa kungiyoyin malaman jami'o'i na CONUA da NAMDA masu kishiyantar ASUU rajista a yunkurin warware matsalolin yajin aiki.

Rajistar wadannan kungiyoyi biyu na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke tattaunawa da ASUU a ci gaba da yajin aikin da kungiyar ke yi.

Yayin bayyana rajistar CONUA da NAMDA, ministan kwadago Chris Ngige ya ce kungiyoyin biyu za su yi aiki kafada da kafada da kungiyar ta ASUU.

Yiwa ASUU kishiya ya saba doka, inji lauyanta

Sai dai, lauyan ASUU Falana ya ce yiwa kungiyoyin biyu rajista ya saba doka. A cewarsa, a bisa doka kungiya daya ce za ta yi aiki a fanni guda, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Yajin-aiki: Kotu Ta Fadawa ASUU da Gwamnati Yadda Za Su Shawo Kan Sabaninsu

A cewar Falana:

"Ba zai yiwu a samu kungiyoyi biyu a fanni daya ba. Kungiya daya ce aka amince da rajistarta a fannin karantarwa a jami'a a Najeriya."

Jami'o'in Najeriya sun kasance a rufe tun watan Fabrairun bana, lamarin da ya jefa daliban Najeriya cikin damuwa.

Jerin Gwamnonin Da Ke Naman Tazarce Zuwa Wa'adi Na Biyu Na Mulki A Zaben 2023

A wani labarin, yayin da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta saki sunayen 'yan takarar gwamna 28 a Najeriya da za su gwabza a zaben 2023, 11 daga cikinsu na neman wa'adi na biyu ne.

A cewar wani rahoton The Nation, an saki wannan jerin sunaye ne a jiya Laraba 5 ga watan oktoba, kuma shine jerin 'yan takara na karshe da INEC ta amince dashi.

Alamu na nuna akwai gwamnonin da za su samu saukin tazarce a zaben mai zuwa, wasu kuwa na da alamar shan fama kafin iya komawa a wa'adi na biyu.

Kara karanta wannan

Minista ya tona asirin wasu gwamnoni, ya ce suna ba tsageru bindigogi AK-47 a lokacin zabe

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.