Isah Barde, Dan Kanon Da Ya Kera Mutum-Mutumi Mai Motsi Da Kwali Ya Samu Tallafin Karatu

Isah Barde, Dan Kanon Da Ya Kera Mutum-Mutumi Mai Motsi Da Kwali Ya Samu Tallafin Karatu

  • Wani hazikin dan Najeriya Isah Barde, wanda ke zaune a Kano ya kera mutum-mutumi mai motsi wanda ya ja hankalin mutane da dama ciki harda gwamnatin tarayya
  • Hukumar NITDA ta baiwa bakanon mai shekaru 17 tallafin karatu kyauta don ya karanci bangaren injiniyan na’ura mai kwakwalwa a jami’ar Baze da ke Abuja
  • Barde ya bayyana cewa wannan somin tabi ne domin yana burin kera manyan mutum-mutumi
  • Ya koka cewa baya samun wasu manyan kayayyaki don cimma kudirinsa na yin manyan kere-kere

Kanowani mazaunin Kano, Isah Barde mai shekaru 17 yana daya daga cikin mutanen da suka ci gajiyar annobar korona, domin wannan ya basu damar yin wasu abubuwa da suka sa su zama shahararru a idon duniya.

Kara karanta wannan

Yadda na kwashe shekaru da dama ina jinyar mijina kan ciwon PTSD, Aisha Buhari

Matashin yak era wani mutum-mutumi ta hanyar amfani da kwali, kuma abun na motsi, BBC Pidgin ta rahoto.

Isah Barde
Isah Barde, Dan Kanon Da Ya Kera Mutum-Mutumi Mai Motsi Da Kwali Ya Samu Tallafin Karatu Hoto: @bbcnewspidgin
Asali: Twitter

Tun tasowarsa Isah ke sha’awar kirkiran abubuwa da kansa. Ya bayyana cewa ya fara kera manyan motocin gona da na gini kafin ya yanke shawarar kera mutum-mutumi.

A wani aji dan Kanon da yak era mutum-mutumi yake?

Kasancewarsa dalibin makarantar sakandare, Isah yace ya samu fasaharsa daga kallon fina-finai da bidiyoyi a yanar gizo. Daga wadannan abubuwan ne ya yanke shawarar fara kera mutum-mutumi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kwanan nan ne Isah ya samu tallafin karatu daga gwamnatin tarayya domin ya karanci injiniyan kwamfuta a jami’ar Baze da ke Abuja, babbar birnin tarayyar Najeriya.

Ya bayyana cewa ya yi amfani da kananan kayayyaki da ake iya samu a koina wajen gina mutum mutumin.

Wa ya baiwa yaron da yak era mutum-mutumin tallafin karatu?

Kara karanta wannan

Shekaru 3 Bayan Mutuwarsa: An Binne Mutumin Da Ya Auri Mata 20 Da Haihuwar Yara Fiye Da 100

Ya dauke shi tsawon shekaru biyu kafin ya kera mutum-mutumin, amma ya ja hankalin mahukunta domin hukumar sadarwa ta kasa NITDA ta bashi tallafin karatu don cimma kudirinsa a rayuwa.

Matashin ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin kalubalen da yake fuskanta shine rashin samun manyan kayayyaki da zai so amfani da su kuma cewa wasu basu aminta da shi ba lokacin da ya fara kera mutum-mutumin.

Isah ya kara da cewa wannan shine somin tabi domin yana shirin kera manyan mutum-mutumi masu inganci.

Kalli bidiyon hirarsa a kasa:

Gidan Duniya: Wata Budurwa Ta Yada Bidiyon Aljannar Duniyar Da Mahaifinta Ya Gina Musu

A wani labarin, wata matashiya yar Najeriya ta je shafin soshiyal midiya domin yada bidiyon katafaren gidan da mahaifinta ya gina masu, wurin har yayi masu girma.

A bidiyon, budurwar ta shiga madafi don nuna famfon da ke fitar da ruwan sanyi da na zafi sannan ta hasko falo daban-daban har guda takwas a cikin gidan.

Kara karanta wannan

Duk Yaudara Ce: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani Ga Bidiyon Atiku Na Tika Rawa Da Na Tinubu Na Tuka Keke

Da take nuno manyan hotuna masu 'dan karen kyau, ta yi barkwanci cewa ta kusa fara siyar da wasu daga cikinsu saboda sun cike ko ina na gidan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng