Shekaru 3 Bayan Mutuwarsa: An Binne Mutumin Da Ya Auri Mata 20 Da Haihuwar Yara Fiye Da 100

Shekaru 3 Bayan Mutuwarsa: An Binne Mutumin Da Ya Auri Mata 20 Da Haihuwar Yara Fiye Da 100

  • Wani mutumin kasar Ghana mai suna Wilson Gbli Nartey daga Ningo ya more rayuwarsa tsaf inda ya mutu yana da shekaru 103 a duniya
  • A cewar rahotanni, mutumin ya auri mata 20 da yara fiye da 110 kuma yana daukar dawainiyarsu su dukka
  • Wani mazaunin garin ya ce marigayin ne ya aiwatar da ayyuka da dama a garin ciki harda gina hanyoyi da kamfanoni

Ghana - Bayan shekaru uku da mutuwarsa, an binne wani mutumin kasar Ghana mai suna Mista Wilson Gbli Nartey daga garin Ningo a yankin Accra. Ya mutu ne a watan Satumban 2019.

An tattaro cewa mutumin mai shekaru 103 a duniya yana da matan aure 20 sannan yana da yara 111 da jikoki fiye da 500.

Wilson Gbli Nartey
An Binne Mutumin Da Ya Auri Mata 20 Da Haihuwar Yara Fiye Da 100 Shekaru 3 Bayan Mutuwarsa Hoto: @joe.anim
Asali: UGC

Babban abun da zai ba mutum mamaki shine yadda majiyoyi suka bayyana cewa Mista Wilson Gbli Nartey ya kula da dukka mata da yaran nasa a lokacin da yake raye. Kuma ya kasance mutum mai kima da mutunci.

Kara karanta wannan

Wani Dan Wasa a Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu Ana Tsaka da Buga Kwallo

A cewar wani mutumin Ningo mai suna Nartey Jokshan, Mista Nartey ya kasance tsohon shugaban kamfanin gine-gine da gishiri na Ghana, kuma har gobe ana cin moriyar manufofinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bugu da kari, mamacin ya gina cibiyar kiwon lafiya a Ningo, ofishin yan sandan Ningo, ofishin aika sakonni na Ningo, kwatas din ma’aikatan Ningo.

Hakazalika ya gina ofishin majalisar yammacin Dangme wanda aka mayar dashi majalisar gargajiya ta Ningo, da kuma kamfanin hada sinadarai na Ningo wanda bai yi nasarar kammalawa ba.

Miliyan N15 Muka Kashe Kan Bikin Aurenmu: Matashiya Yar Najeriya Ta Wallafa Hotuna Da Bidiyoyi

A wani labarin, wata matashiya yar Najeriya, Jessica Ayodele, ta je shafin soshiyal midiya a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba don bayyana makudan kudaden da ta kashe a kan aurenta.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Gano Gawar Wata Mata a Ofishin Shugaban Wani Babban Asibitin Arewa

Matar ta bayyana cewa daga ita har mijinta sun kashe zunzurutun kudi har naira miliyan 15 a kan kasaitaccen bikin aurensu.

Jessica ta bayyana cewa a lokacin da suke shirye-shiryen aurensu a watan Afrilu, duk tunaninta ba za su kashe kudi fiye da naira miliyan 5 ba wajen gayyatar mutane 100 kacal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel