Gidan Duniya: Wata Budurwa Ta Yada Bidiyon Aljannar Duniyar Da Mahaifinta Ya Gina Musu

Gidan Duniya: Wata Budurwa Ta Yada Bidiyon Aljannar Duniyar Da Mahaifinta Ya Gina Musu

  • Wata matashiya yar Najeriya ta baje kolin katafaren gidan hamshakin mahaifinta wanda ke da komai na more rayuwa a ciki
  • A cikin katafaren gidan, akwai dakin sama da ba a cika amfani dashi ba, akwai kuma babban wurin shakatawa; wanda sai a gidan hamshakai ake ganin irinsu
  • Yan Najeriya da dama da suka yi martani ga bidiyon cike da barkwanci sun ce zasu so ace ana rikonsu a wannan babban gida

Wata matashiya yar Najeriya ta je shafin soshiyal midiya domin yada bidiyon katafaren gidan da mahaifinta ya gina masu, wurin har yayi masu girma.

A bidiyon, budurwar ta shiga madafi don nuna famfon da ke fitar da ruwan sanyi da na zafi sannan ta hasko falo daban-daban har guda takwas a cikin gidan.

Gidan manya
Gidan Duniya: Wata Budurwa Ta Yada Bidiyon Aljannar Duniyar Da Mahaifinta Ya Gina Musu Hoto: TikTok/@craxyxeey
Asali: UGC

Falo takwas, dakin sama da wutar Solar

Kara karanta wannan

Dan Achaba Ya Baje Kolin Dankareren Gidan Da Ya Ginawa Mai Shirin Zama Amaryarsa, Hoton Ya Ja Hankali

Da take nuno manyan hotuna masu 'dan karen kyau, ta yi barkwanci cewa ta kusa fara siyar da wasu daga cikinsu saboda sun cike ko ina na gidan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A saman rufin gidan an gano na’urar sola wanda ke nuna gidan na samun wuta ne daga hasken rana ba wai sun dogara da gwamnati ta basu lantarki bane.

Akwai wani dakin hutu a sama da ahlin basu cika amfani da shi ba. Mutane da dama sun ce lallai budurwar ta fito ne daga babban gida na masu hannu da shuni.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

Dinmahelen ta ce:

“Shin an gayyace ni, ba zan ketare iyaka ba nayi alkawari.”

Mirall ta ce:

“Wannan shine fadamun kina da kudi ba tare da kince kina da kudi ba.”

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

Kamso ta ce:

“Yar mai kudi. Da yardarm Allah yarana za su samu wannan damar Amin.”

Aliyu Zhara Saeed ta ce:

“Bari na fara hada kayayyakina.”

Dan Achaba Ya Baje Kolin Dankareren Gidan Da Ya Ginawa Mai Shirin Zama Amaryarsa, Hoton Ya Ja Hankali

A wani labarin, wani dan achaba mai suna Kahii Ga Cucu ya burge jama’a a soshiyal midiya bayan ya nuna wani dankareren gida da ya kerawa kansa.

Da ya je wani shafin Facebook mai suna Dream House and Building Forum don wallafa hoton gidan nasa, mutumin ya nuna farin cikin mallakar gida sukutum duk da irin fadi tashin da yake yi wajen samun na kai.

Ya bayyana cewa gidan nasa ne shi da wacce za ta zama matarsa a gaba sannan ya tunatar da jama’a cewa kowani irin kasuwanci yana da amfani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel