Yajin-aiki: Kotu Ta Fadawa ASUU da Gwamnati Yadda Za Su Shawo Kan Sabaninsu
- Kungiyar malaman jami’a watau ASUU sun daukaka kararsu da gwamnatin tarayya a babban kotu
- Da aka zauna a kotun daukaka kara, Georgewill Abraham ya bukaci bangarorin suyi sulhu da junansu
- Alkali yana sa rai nan da gobe a ji an sasanta tsakanin Gwamnati da kungiyar ASUU, a jefar da karar
Abuja - Babban kotun daukaka kara da ke zama a birnin tarayya na Abuja ta saurari karar da kungiyar ASUU ta shigar a kan gwamnatin tarayya.
Rahoton da ya fito daga gidan talabijin na Channeles TV yace Alkali fadawa kungiyar malaman jami’a da gwamnatin tarayya su sasanta wajen kotu.
Babban lauyan da ya tsayawa kungiyar ASUU, Femi Falana (SAN) da James Igwe (SAN) mai kare gwamnatin tarayya sun halarci zaman da aka yi dazu.
Mai shari’a Georgewill Abraham ya bada shawara ga bangarorin biyu su zauna da junansu domin su cin ma matsaya a kan abin da zai ceci ‘yan Najeriya.
The Cable ta rahoto Alkalin yana fadawa lauyoyin da suka tsayawa ASUU da gwamnati su zauna a kan tebur nan da awa 24 domin a samu maslaha.
Komai da lokacinsa - Alkali
“Akwai lokacin komai; akwai lokacin fada, akwai na zaman lafiya.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“A matsayinku na manya a gidan shari’a, muna so ku biyu ku zauna tun da ku manyan lauyoyi ne, ku bada shawarar a samu maslaha a wannan rikici.”
“Kai muna so a dawo zaman kotu ranar Alhamis dinnan da labari mai dadi cewa an dinke barakar, idan aka yi haka, duk ‘Yan Najeriya za su gode maku.
“Saboda haka ku yi magana da wadanda ku ke karewa, su duba kishin kasa da halin yaranmu. Idan kun bar nan, ku je ku zauna domin shawo kan batun.”
Punch ta rahoto James Igwe da Femi Falana sun amince za su bi shawarar Alkali Abraham, za suyi kira ga bangarorin malamai da gwamnati su koma tebur.
Idan Nayi Nasara Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arziki Kasar, Kwankwaso Ya Yi Alkawari
Hushpuppi zai je kurkuku?
Mun ji labari Ramon Abbas watau ‘Hushpuppi’ ya nemi a yanke masa hukunci mara tsauri sosai saboda ya ba jami’an tsaro hadin-kai a kasar Amurka.
Amma Lauyoyin Gwamnatin kasar ta Amurka da suka shigar da kara sun ce akwai bukatar Hushpuppi ya yi shekaru 11 yana tsare a makargama.
Asali: Legit.ng