Katsina: An Kama Matar Aure Yar Shekara 20 Kan Kashe Yar Kishiyarta Jinjira Yar Wata Bakwai

Katsina: An Kama Matar Aure Yar Shekara 20 Kan Kashe Yar Kishiyarta Jinjira Yar Wata Bakwai

  • Yan sanda sun kama wata matar aure yar shekara 20 mai suna Lamratu kan kisar jinjirar kishiyarta yar wata bakwai a Katsina
  • Dan sanda mai gabatar da kara ya shaidawa kotu cewa lamarin ya faru ne a kauyen Unguwar Shalele a ranar 21 ga watan Agusta
  • Bayan sauraron korafin, dan sandan ya bukaci a bashi dama ya kammala bincike, kotu ta amince amma ta ce a ajiye Lamratu a gidan gyaran hali

Jihar Katsina - Kotu ta bada umurnin a tsare mata wata matar aure, yar shekara 20, Lamratu Nasiru, a gidan gyaran hali kan kashe yar kishiyarta, The Punch ta rahoto.

An rahoto cewa Lamratu ta doki jinjirara yar wata bakwai ne a kai da sanda yayin da suke rikici da mahaifiyarta, Zabbau Nasiru.

Taswirar Katsina.
An Kama Matar Aure Yar Shekara 20 Kan Kashe Yar Kishiyarta A Katsina. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Lamratu da Zabbau matan wani Malam Nasiru ne a Kauyen Unguwar Shalele da ke karamar hukumar Matazu na jihar Katsina.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a Sun Maka IGP da CMD Kotu, Sun Bukaci Alkali Ya Jefa su Kurkuku

Yan sandan sun kara da cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Sakamakon hakan, jinjiran ta samu rauni mai tsanani a kanta aka kuma garzaya da ita babban asibiti da ke Musawa, inda likita ya tabbatar ta rasu."

Yan sanda: Yadda Lamratu ta halaka yar kishiyarta

Lauyan Yan sanda a Katsina ya shaidawa babban kotun Majistare inda aka shigar da karar cewa lamarin ya faru ne a ranar 21 ga watan Agustan 2022 a kauyen Unguwar Shalele.

Zubbau ce ta kai kara ofishin yan sanda da ke Matazu, bayan hakan aka kama Lamratu aka kai ta kotu.

Yan sanda suna son a kama Lamratu da laifin kisa bisa sashi na 189 na dokar Penal Code ta Jihar Katsina, 2021.

An kuma shaidawa kotun cewa ita ma mahaifiyar jinjiran, Zabbau ita ma ta samu rauni sakamakon rikicin.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Sani Ado, ya fada wa kotu cewa ana cigaba da bincike kan lamarin, ya roki a sake basu wani ranar sauraren karar.

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

Kotu ta ce a bawa Lamratu masauki a gidan yari

Alkaliyar, Hajiya Fatima Fadile Dikko ta amince da bukatar inda ta dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Oktoban 2022.

Ta umurci a tsare Lamratu a gidan gyaran hali na Katsina har zuwa ranar da za a saurari shari'ar.

An damke fasto da ta sace jinjira a Akwa Ibom

A wani rahoton, Rundunar yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce ta kama wata Mrs Mmayen Odiuotip, mai shekaru 39 fasto a cocin Land of Testimony Ministry a kan zarginta da satar jinjira.

Cocin yana Marina Road ne a karamar hukumar Oron na jihar kamar yadda The unch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164