An damke fasto da ta sace jinjira a Akwa Ibom

An damke fasto da ta sace jinjira a Akwa Ibom

Rundunar yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce ta kama wata Mrs Mmayen Odiuotip, mai shekaru 39 fasto a cocin Land of Testimony Ministry a kan zarginta da satar jinjira.

Cocin yana Marina Road ne a karamar hukumar Oron na jihar kamar yadda The unch ta ruwaito.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, CSP Nnudam Fredrick, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a babban birnin jihar, Uyo.

Ya ce wasu da ake zargi da hannu cikin satar yaran sun hada da Esther Esin, 41 yar garin Eyo Abasi, a karamar hukumar Oron, Mrs Rose Asuquo, 32, yar garin Mbak Atai, karamar hukumar Itu, da Ubong Akpan, 42, dan garin Mbak Atai, daga karamar hukumar Itu.

An kama fasto saboda satar jarirai a Akwa Ibom
An kama fasto saboda satar jarirai a Akwa Ibom
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Uganda: Matashi ɗan shekara 19 ya fito takarar shugaban kasa

Saura sun hada da Mr Samuel Idobo, 40, mazaunin Ikot Asukpong, a karamar hukumar Ibiono Ibom da Mrs Eno Peter, 40, yar garin Ikot Andem Itam, da ke karamar hukumar Itu.

"Jajircewar da rundunar yan sandan ke yi domin magance matsalar satar yara ya fara samun nasara inda aka damke gawurtattun masu satar yara a jihar," in ji Fredrick.

Fredrick ya ce an yi nasarar kama yan kungiyar masu satar yaran ne sakamakon sahihan bayannan sirri da rundunar ta samu a watan Yuni.

Ya ce shugaban kungiyar, Rose Ekpenyong, ta hada baki da sauran wadanda ake ambaci sunansu a matsayin wadanda ake zargi wurin sayar da wata jinjira a shekarar 2018.

Fredrick ya ce faston ta amsa laifin ta inda ta ce an saya jinjiran ne domin a bawa yar uwar ta mai suna Esin.

"Hakan ya sa jami'an hukumar suka bazama suka kamo ta sannan suka ceto jinjirar," in ji shi.

Fredrick ya yi kira da alumma su cigaba da taimakawa rundunar da bayanai masu amfani da za su taimaka musu wurin kama masu satar yara da safarar su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel