Yadda Za Mu Sha Bam-Bam da ‘Yan ASUU Inji Kishiyar Kungiyar Malaman Jami’a
- ‘Yan kungiyar malaman jami’a na Congress of Nigerian University Academics sun bayyana manufofinsu
- Shugaban CONUA yana ganin yajin-aiki irin na ASUU ba zai haifar da mai ido ba, dole a sake yin nazari
- Dr. Niyi Sunmonu yana ganin malaman jami’a suna tursasa gwamnati ne shiyasa aka gaza cika alkawura
Abuja - Kungiyar Congress of Nigerian University Academics ta ma’aikatan jami’a da suka balle daga ASUU tayi bayanin matsayar da za su dauka.
Shugaban CONUA na kasa, Dr. Niyi Sunmonu ya yi hira da gidan talabijin na Arise, ya yi bayanin yadda kungiyarsu za ta banbamta daga ASUU.
Dr. Niyi Sunmonu yace za su bi wata hanya dabam domin kawo karshen yajin-aikin da ake yawan yi, wanda yanzu ya jawo dalibai suke zaman gida.
A cewar shugaban sabuwar kungiyar, ya kamata malaman jami’a suyi wa lamarin kallo na dabam, a canza yadda ake gudanar da abubuwa a jami’o’i.
Kullum ana ta abu daya - CONUA
Sunmonu yace babu dalilin da malamai za su kafe a kan matsayarsu, su hau kujerar na-ki alhali akwai wasu hanyoyi da za a iya bi wajen samun maslaha.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Malamin jami’ar wanda yake jagorantar tafiyar CONUA a kasar nan yake cewa an dauki kimanin shekaru 40 ana yajin-aiki a jam’o’in gwamnatin kasar.
Dr. Sunmonu yana ganin a karshe kungiyar ASUU tana tursasawa gwamnatin tarayya ta sa hannu a yarjejeniyar da ba za a cika ba, sai a saba alkawari.
Ko a yaki, ana zama domin bangarori su sasanta, saboda haka kungiyar take ganin babu abin da zai hana ayi zama da kyau domin samun mafitar kwarai.
A karshe yara suke shan wahala
Malamin jami’ar yake cewa wadanda suke shan wahala a yanayin da ake ciki su ne dalibai da iyayensu, don haka suke neman yadda za a ceci kowanensu.
“Muna ganin cewa ana cin ma wannan yarjejeniya ne da karfi da yaji”
- Dr. Niyi Sunmonu
CONUA tana so gwamnati ta zo hankali kwance ta sa hannu a yarjejeniya da zarar an cin ma matsayar za ta iya aiki, ba a tursasa bangaren gwamnati ba.
An yi wa CONUA rajisa
An ji labari Gwamnatin Muhammadu Buhari tayi wa wasu ƙungiyoyin malaman jami'a rajista. Ana tunanin wannan zai iya rage karfin 'Yan ASUU.
Tun a farkon shekarar nan Ƙungiyar Malaman Jami'a ta ƙasa (ASUU) ta tsunduma yaƙin aiki, kuma har zuwa yau an gagara shawo kan matsalar nan.
Asali: Legit.ng