Gwamnatin Tarayya Ta Karya Lagon ASUU, Ta Yiwa Kishiyoyinta Biyu Rijista

Gwamnatin Tarayya Ta Karya Lagon ASUU, Ta Yiwa Kishiyoyinta Biyu Rijista

  • Tun a watan Fabrairu ne malaman Ƙungiyar Malaman Jami'a ta ƙasa (ASUU) ta zunduma yaƙin aiki
  • Kuma an sha zama domin ganin an warware matsalar, amma abin ya citura.
  • Sannan ta sa yanzu ake ganin gwamantin ta karya lagwanso bayan yi musu kishiyoyi har gida biyu.

A wani abu da ake kallo a matsayin karya alƙadarin Ƙungiyar Malaman Jami'an ta Ƙasa (ASUU), gwamantin tarayya, a ranar Talatan nan, ta yi wa ƙungiyar kishiyoyi bayan da ta yi wa wasu ƙungiyoyi biyu rijista da suka shafi ma'aikatan jami'a a Najeriya.

Ƙungiyoyin sun haɗa da: Ƙungiyar Malaman Sashen Cuta da Magani da Haƙora (National Association of Medical and Dental Academics) da za a fi sani da (NAMDA) da kuma Gamayyar Ƙungiyar Malaman Jami'a ta Ƙasa, wato Congressversity Academics (CONUA).

Kara karanta wannan

Muhimmin Abun Da Zan Yi Idan Na Ɗare Kujerar Shugaban Ƙasa a Zaɓen 2023, Kwankwaso

An kafa CONUA ne tun a shekarar 2018 a ƙarƙashin wata jami'ar jihar Osun wanda ita ayyukanta zai kasance irin na ASUU.

Ngoge
Gwamnatin Tarayya Ta Karya Lagon ASUU, Ta Yiwa Kishiyoyinta Biyu Rijista
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan Ma'aikata, Chris Ngige, ne ya bayyana hakan tare da tabbatar da cewa ƙungiyoyin za su yi kafaɗa-da-kafaɗa da taƙwararsu ta ASUU.

Sai dai wannan yunƙuri ya gamu da ka-ce-na-ce tun bayan da aka bayyana hakan kamar yadda mutane suka bayyana a shafin ɗaya daga cikin hadiman shugaba Buhari, Bashir Ahmad a dandalin sada zumunta na Twitter.

Wasu dai na ganin baiken gwamantin musamman na ƙoƙarin cika wa ƙungiyar buƙatunta. Wasu kuwa na ganin ai maganar banza ce idan aka yi duba da irin yadda hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba ga cigaban ilimi a ƙasa bakiɗaya.

Idan za a iya tunawa dai, ASUU ta tafi yaƙin aiki ne tun 14 ga watan Fabrairu, 2022 saboda nuna rashin amincewarsu ga ƙungiyoyin biyan wasu kuɗaɗe na alawus-alawus da kuma nuna buƙatar inganta rayuwarsu daga gwamnatin tarayyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel