Hukumar NCDC Ta Gargadi Najeriya Kan Hadarin Barkewar Cutar Ebola

Hukumar NCDC Ta Gargadi Najeriya Kan Hadarin Barkewar Cutar Ebola

  • Hukumar kula da cututtuka masu harbuwa ta NCDC ta gargadi 'yan Najeriya bisa hasashen bullar cutar Ebola a kasar a nan gaba kadan
  • Hukumar ta samu labarin yadda kasar Uganda ta ayyana bullar cutar Ebola, kana ta sanar da adadin mutanen da suka kamu da wadanda suka mutu
  • NCDC ta ba da matakan kariya a matakin farko domin kaucewa kamuwa da cutar da kuma yaduwarta, ta ba da lambar waya

Hukumar kula da cututtuka masu harbuwa (NCDC) ta ce Najeriya na cikin hadari sake shigo da cutar Ebola daga kasar Uganda, TheCable ta ruwaito.

Kasar Uganda ta ayyana barkewar cutar Uganda bayan da wani matashi mai shekaru 24 ya fara mashassharar cutar kana ya mutu daga bisani.

Akwai yiwuwar Ebola ta barke a Najeriya
Hukumar NCDC Ta Gargadi Najeriya Kan Hadarin Barkewar Cutar Ebola | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Ya zuwa ranar 29 ga watan Satumba ma'aikatar lafiya a kasar Uganda ta ce akalla mutane 54 ne suka kamu da cutar, an ce 25 sun mutu.

Kara karanta wannan

Jama'a sun shiga mamaki, dalibar jami'a a Najeriya ta haifi jarirai 5 nan take

Matsayar Najeriya kan wannan hasashe

Duk da haka, hukumar ta ce gwamnatin Najeriya na da duk abubuwan da ake bukata wajen dakilewa da rage yaduwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bangare guda, hukumar ta gargadi 'yan Najeriya da su guji tafiye-tafiye marasa dalili zuwa kasashen da ke cutar a yanzu.

Hakazalika, ta ce mutane su guji cudanya ta kai tsaye da jama'a domin kaucewa yaduwar cutar.

Daga karshe, ta ba da lambar waya domin a kira ga duk wanda ya ji alamar cutar a jikinsa, ta ce za a iya kiran wannan lamba (6232) domin ba da rahoton cutar.

NCDC ta gargaɗi ƴan Nigeria kan yiwuwar sake ɓullar Ebola

A wani labarin na daban kuma, cibiyar Kare Cututtuka Masu Yaduwa, NCDC, ta ce akwai yiwuwar annobar Ebola za ta iya sake bulla a Nigeria kamar yadda ta wallafa a shafinta na intanet.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hukumar 'yan sanda ta kori wasu manyan jami'anta 7, ta ragewa 10 girma

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta tabbatar da babu Ebola a Nigeria a ranar 20 ga watan Oktoban 2014 bayan wani dan kasar Liberia, Patrick Sawyer ya shigo da cutar cikin kasar.

Cutar ta yi sanadin rasuwar yan Nigeria da dama cikinsu har da Dr Stella Adadevoh wacce ta kula da Sawyer sannan ta hana shi barin asibitin Legas inda aka kwantar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.