Shugaba Buhari Ya Samu Karuwa, Jikarsa Ta Haifa Masa Tattaba Kunne

Shugaba Buhari Ya Samu Karuwa, Jikarsa Ta Haifa Masa Tattaba Kunne

  • Iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari sun samu karuwa, sun samu tattaba kunne ta farko
  • Jikar shugaban kasar, Aisha Mukhtar wacce ta aure Khalid Wambai a shekarar bara ta haifi kyakkyawar diyarta mace
  • Aisha diyace a wajen ‘yar shugaban kasar ta biyu, Hajiya Fatima, kuma matarsa ta farko marigayiya Safinatu ce ta haife ta

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu karuwa a cikin iyalinsa, inda aka haifa masa tattaba kunne ta farko.

Iyalan shugaban kasa
Shugaba Buhari Ya Samu Karuwa, Jikarsa Ta Haifa Masa Tattaba Kunne Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa jikar shugaban kasar, Aisha Muktar wacce ta auri Khalid Wambai a shekarar 2021 ta santalo kyakkyawar diyarta mace.

Aisha ta kasance diya ga Hajiya Fatima, ‘yar shugaban kasa Buhari ta biyu kuma mamba a hukumar CIFCFEN.

Hotunan Wankan Ranar Zagayowar Samun ‘Yancin Kai na Iyalan Shugaba Buhari Sun Kayatar

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranar Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

A wani labarin kuma, hotunan iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari sun matukar kayatarwa na ranar shagalin bikin zagayowar ranar samun 'yancin kan Najeriya karo na 62.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Iyalan sun yi shigar sutturu launin fari da kore inda suka matukar fitowa suka yi kyau yayin da suka je har filin wasa na Eagle Square.

Kamar yadda @fashionseriesng suka wallafa kyawawan hotunan iyalan, an ga Halima Buhari Babagana da maigidanta, Zarah Buhari Indimi da mijinta Ahmad, Hanan Buhari da angonta Muhammad Turad duk sun fito gwanin sha'awa a filin wasa ana Eagle Square dake Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng