Boyayyun Hadimai 11 da ke Cikin Aso Rock Villa da Aikin da Kowa Yake Yi wa Buhari
- Akwai wasu daga cikin Hadiman shugaban kasa da mutanen Najeriya da-dama ba su san da zamansu ba
- Masu taimakawa Mai girma Muhammadu Buhari sun hada da Likitoci har zuwa masu kula da cikin dakinsa
- Daga cikin wadanda suke aiki a fadar shugaban Najeriyan akwai Masu daukarsa hotuna a duk inda ya shiga
Mun tattaro jerin Hadiman shugaban kasar kamar yadda aka fitar da sunayensu a lokacin da aka sake nada su a Mayun 2019.
1. Mohammed Sarki Abba
Babban Mai taimakawa shugaban kasa na musamman a kan harkokin gida da taron jama’a.
2. Ya’u Shehu Darazo
Babban Mai taimakawa shugaban kasa na musamman a kan ayyuka na musamman.
3. Dr. Suhayb Sanusi Rafindadi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Likitan da ke kula da lafiyar Mai girma shugaban kasa.
4. Amb. Lawal A. Kazaure
Mai kula da tsare-tsaren fadar Shugaban kasa
5. Sabiu Yusuf (Tunde)
Mai taimakawa na musamman (a ofishin shugaban kasa).
6. Saley Yuguda
Mai taimakawa na musamman (a wajen kula da gida).
7. Ahmed Muhammed Mayo
Mai taimakawa na musamman (a wajen tattalin kudi da gudanarwa).
8. Mohammed Hamisu Sani
Mai taimakawa na musamman (a wajen ayyuka na musamman).
9. Friday Bethel
Mai taimakawa Shugaban kasa (Ayyukan yau da gobe).
10. Sunday Aghaeze
Mai taimakawa wajen daukar hoto a fadar Shugaban kasa
11. Bayo Omoboriowo
Mai taimakawa wajen daukar hoton Mai girma Shugaban kasa
Sauran masu aiki a Aso Villa
Wannan jeri bai kunshi masu magana da yawun bakin Muhammadu Buhari da sauran wadanda suke taimaka masa wajen harkokin ofishinsa ba.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasan gaba daya shi ne Farfesa Ibrahim Gambari wanda ya canji Malam Abba Kyari bayan rasuwarsa a 2020.
Asali: Legit.ng