Lambar Girma: Yadda Ake Surutu Yayin da Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi
- A mako mai zuwa ake sa rai Gwamnatin tarayya za ta bada lambobin karramawa ga wasu da suka yi fice
- Zuwa yanzu sam wannan ba sabon labari ba ne, sabon labari shi ne ana suka kan wadanda za a ba lambobin
- Muhammadu Buhari zai karrama wasu na kusa da shi irinsu manyan hadimansa da masu taya shi aiki
Abuja - A rahoton da Punch ta fitar, an ji akwai masu korafi saboda sun fahimci irin mutanen da gwamnatin Muhammadu Buhari za ta ba lambar girma.
Kungiyoyi masu zaman kansu sun koka da cewa ‘yan siyasa suka ciki jerin sunayen da aka gani, alhali akwai sauran ‘Yan Najeriya da suka dace da lambar.
Shugaban kungiyar YIAGA, Samson Itodo yace Mai girma shugaban kasa yana da damar ya karrama wadanda yake ganin sun kawowa kasa nasarori.
Amma Itodo yace ya kamata a zakulo mutanen da suka zama abin koyi ne ga sauran jama’a.
Itodo ya tuhumi gwamnatin Buhari da raba wadannan lambobi da su ne mafi girman yabo a Najeriya ga wasu wadanda ake ganin akwai kashi a gindinsu.
Ina aka bar Bukola Saraki?
Dare-Ariyo Atoye wanda yake jagorantar Coalition in Defence of Nigerian Democracy and Constitution mai kare tsarin mulki ya soki yadda aka yi abin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dare-Ariyo ya soki gwamnati musamman ganin yadda aka ki sa Bukola Saraki a cikin wadanda za a karrama duk da kuwa ya rike shugaban majalisa.
Surukai da Hadimai sun samu shiga
A sahun wadanda za a karrama akwai Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero wanda zai samu lambar CFR. Mai martaban suruki ne a wajen Muhammadu Buhari.
Haka zalika za a bada lambar OON ga Dr. Sanusi Rafindadi wanda shi ne likitan shugaban kasa.
Wani na kusa da fadar shugaban kasa da sunansa ya fito shi ne Femi Adesina. Hadimin da zai samu OON shi ne magana da yawun Buhari tun 2015.
Wasu sun soki lamarin ne saboda ganin sunan Mamman Daura. An ware Kawun shugaban Najeriyan za a ba shi lambar CON a matsayin dattijon kasa.
Har ila yau Sarki Abba da Tunde Yusuf Sabiu za su samu OON. Duka wadannan mutane suna da kusanci da Mai girma shugaban kasa da fadarsa.
Abdulhalim Ringim yace idan za a zabi irinsu Yusuf Sabiu, ya kamata a karrama Prince Muhammad Kadade wanda matashi ne da ya yi fice a siyasa.
Bashir Yusuf Jamoh wanda surukin matashin hadimin shugaban kasar ne ya shiga jerin. ‘Danuwan shugaban kasar yana aure diyar shugaban NIMASA.
Sauran hadiman da ke jerin su ne Janar Babagana Munguno (rtd) da Ahmad Rufai.
Za a karrama Abba Kyari
Kun ji labarin wadanda za a ba lambobin yabo sun hada da ‘yan siyasa, ma’aikata, jami’an tsaro da fitattun ‘yan kasuwa, daga ciki har da Marigayi Abba Kyari.
Kyari ya rike kujerar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa har ya rasu. A jerin akwai malaman addini da wasu mutanen kasar waje da suka kawo cigaba.
Asali: Legit.ng