An Kama Shugaban Autonation Motors, Nsofor Chukwukadibia da Laifin Mallakar Kwayoyin Tramadol
- A ranar Litinin 3 ga watan Oktoba ne hukumar NDLEA ta sanar da kwamushe wasu kayayyakin Tramadol a jihar Legas
- A cewar hukumar, katafaren gidan da aka gano kwayoyin mallakin shugaba kamfanin Autonation Motors, Ugochukwu Nsofor Chukwukadibia
- Biloniyan dan yankin Kudu maso Yammcin Najeriya ya tara katan 443 na kawayoyin Tramadol Hydrochloride masu girman 225mg da ke dauke da kwayoyi 13, 451,466
Legas - An kama biloniya kuma shugaban kamfanin Autonation Motors Ugochukwu Nsofor Chukwukadibia bisa gano ya mallaki kwayoyin Tramadol miliyan 13.4 a wani katafaren gini da ke Victoria Garden City a jihar Legas.
Hukumar NDLEA ta sanar da wannan lamari ne a ranar Lirinin 3 ga watan Oktoba a Lekki ta jihar Legas, PM News ta ruwaito.
A cewar mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafeni, an kama kayayyakin Tramadol da suka kai darajar akalla N8.86bn a ginin.
Kamun nasa na zuwa ne watanni biyu kacal bayan da NDLEA ta bankado wani dakin kwaje-kwaje na sinadaran methamphetamine clandestine a gidan wani kasurgumin dan harkallar kwayoyi a unguwar mai suna Chris Emeka Nzewi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An gano motoci masu tsada a gidan Ugochukwu
A cewar Babafemi, an kama manyan motoci masu tsada a katafaren gidan Chukwukadibia, kuma biyu daga cikin motocin SUV ne har da motar da ba ta jin harbin harsashi.
Ya kuma bayyana cewa, tuni hukumar ta tattara komai zuwa ofishinta domin ci gaba da bincike.
Sanarwar da hukumar ta fitar a shafinta na Twitter ya bayyana dalla-dalla irin kayayyakin da aka tattaro daga gidan wannan biloniya a Kudu maso Yammacin Najeriya.
Hukumar NDLEA n ci gaba da sa jiki wajen kame masu safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.
Ku Yi Hattara da Macewar Sassan Jiki da Ciwon Daji, NAFDAC Ta Gargadi Masu ‘Bleaching’
A wani labarin, hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta gargadi 'yan Najeriya game da amfani da kayan kwalliya da sinadarai masu hadari wajen kwaile fata don kara kyau.
Wannan na fitowa ne a jiya Lahadi 25 ga watan Satumba daga bakin babban daraktan hukumar, Farfesa Majisola Adeyeye a wani taron kwana biyu da hukumar ta shirya a Legas.
Ta yi gargadin cewa, sinadaran da ke tattare layan kwaile fata na dauke da ababen da ke sa cutar daji a fatar dan-adam, ya lalata gabobi har ma ya kai ga mutuwa, inji rahoton Daily Trust.
Asali: Legit.ng