ASUU: Gwamna Tambuwal Ya Fusata, Ya Dakatar Da Albashin Malaman Jami'a

ASUU: Gwamna Tambuwal Ya Fusata, Ya Dakatar Da Albashin Malaman Jami'a

  • Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, yace ya dakatar da biyan malaman jami'ar jihar Albashi
  • Gwamnan a wurin wani taron matasa, yace bai ga dalilin da zai sa malaman su ci gaba da yajin aiki ba domin ba su da matsala da gwamnati
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya yaba wa gwamnan bisa kokarin jawo matasa a cikin gwamnatinsa

Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya dakatar da biyan Malaman Jami'ar jiharsa da suka shiga yajin aiki, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) ta ayyana shiga yajin aiki tun a watan Fabrairun wannan shekarar kan bukatun inganta walwalar Lakcarori da sauransu.

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto.
ASUU: Gwamna Tambuwal Ya Fusata, Ya Dakatar Da Albashin Malaman Jami'a Hoto: dailytrsut.com
Asali: UGC

Duk wani yunƙurin gwamnatin tarayya na ganin Malaman sun janye sun koma aji bai kai ga nasara ba har zuwa yau.

Kara karanta wannan

Ku yi hakuri: Gwamnati ta yi laushi, ta fara lallabi da rokon ASUU ta janye yaji

Yayin da yake jawabi ga matasa a International Conference Centre, Kasarawa a ƙarshen makon nan, Gwamna Aminu Tambuwal ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A watan da ya gabata na dakatar da biyansu Albashi saboda na yi musu alfarmar da zan iya na biyansu Albashi tsawon watanni biyar ba tare da sun yi aikin komai ba."
"Na faɗa musu su koma aiki ko kuma su rasa albashinsu saboda ba su da wani dalili da zasu ci gaba da wannan yajin aikin. Batun da rassan ASUU na jami'o'in tarayya suka ɗaga ba daya yake da na jami'ar jiha ba."
"Idan suna da wata matsala su gabatar mana da su, idan kuma ba haka ba to tabbas ba zamu biya su albashi ba har sai sun koma aji."

Gwamnan ya buƙaci Malaman Jami'ar jihar su koma bakin aiki indai dagaske suna da sha'awar cigaban jihar Sakkwato da ɗalibanta a zuciyoyinsu.

Kara karanta wannan

2023: Ba Zan Bar 'Ya'Yana Su Fita Zuwa Ƙasashen Waje Ba, Atiku Ya Ɗau Sabbin Alƙawurra

An yaba wa Tambuwal kan tafiya da matasa

A nasa jawabin, kwamishinan yaɗa labarai wanda ke kula da ma'aikatar matasa da ci gaban wasanni, Akibu Ɗalhatu, ya yaba wa gwamnan bisa tafiya da matasa a jihar ta hanyar kirkiro shirin tallafi daban-daban da suka ci gajiya.

Bugu da ƙari kwamishinan ya yaba wa gwamna Tambuwal bisa jawo matasa da ba su muƙamai a ɓangarori da dama na gwamnatinsa.

A wani labarin kuma Dan takarar shugaban kasa ya fadi abu daya zai yi ya magance yajin ASUU

Farfesa Christopher Imumolen ya bayyana kadan daga irin abin da ya shirya don gyara fannin ilimi da ya gurbace a Najeriye.

Dan takarar na jam'iyyar Accord ya ce a karkashin kulawarsa, dole zai sauya kowane fanni a ma'aikatar ilimin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262