Matashi Ya Zana Katafaren Hoton Peter Obi Jikin Bango A Jihar Kaduna, Yan Najeriya Sun Yi Martani

Matashi Ya Zana Katafaren Hoton Peter Obi Jikin Bango A Jihar Kaduna, Yan Najeriya Sun Yi Martani

  • Wani hazikin matashi mai suna Bamaiyi Danladi ya zana katafaren hoton dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, a jikin bango a Kaduna
  • Bamaiyi ya sanyawa dan takarar shugaban kasar hulan jan-dara irin na yan Igbo sannan yana dauke da murmushi a fuskarsa wanda ya kara masa tsari
  • Yan Najeriya da suka kalli bidiyon yadda aka fara zanen har zuwa karshe sun jinjinawa matashin

Wani matashi dan Najeriya da ya shahara wajen yin zanen hotuna iri-iri, Bamaiyi Danladi, ya je shafin intanet don baje kolin wani hadadden aiki da yayi a Kaduna.

A wani bidiyo da ya yadu, matashin ya zana wani katafaren hoton dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, a jikin wani bango a jihar.

Zanen Peter Obi
Matashi Ya Zana Katafaren Hoton Peter Obi Jikin Bango A Jihar Kaduna, Yan Najeriya Sun Yi Martani Hoto: TikTok/@bamaiyidanladi
Asali: UGC

Ya nuna yadda ya fara zanen har zuwa karshen hoton. Wannan baiwa tasa ta burge yan Najeriya da dama.

Kara karanta wannan

Nigeria @62: 'Yan Najeriya Sun Gaji Da Shugabannni Gajiyayyu masu gajiyawa, Peter Obi

Da ya bukaci masu amfani da soshiyal midiya su bayyana ra’ayinsu game da aikinsa, mutane da dama sun sanyashi a babban mizani na 1 zuwa 10.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli bidiyonsa a kasa:

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, bidiyon ya tara martani fiye da 300 da ‘likes’ sama da 4000.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

boss_sheriff1 ya ce:

“Ka kware dan uwa.”

uzom123 ya ce:

“Ka yi kokari sosai.”

user5493746449524 ya ce:

“Na baka 9, daga mizanin 1 zuwa 10.”

Faustinaclare10 ya ce:

"100/10."

chikamsodavid ya ce:

“Na rantse Peter obi zai hada kan Igbo da hausawa. Muna addu’an haka.”

Buhari Zai Karrama Sarkin Kano, Sarkin Zazzau Da Wasu Sarakuna 18 Da Lambar Girma Ta Kasa

A wani labarin, an saki jerin sunayen mutanen da gwamnatin Najeriya za ta karrama da lambar girmamawa ta kasa na wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Matashi Dan Shekaru 20 Ya Auri Matashiyar Budurwa, Bidiyon Aurensu Ya Haddasa Cece-kuce A Intanet

Legit.ng ta rahoto cewa mutane 437 ne za su samu lambar yabo daga bangarori daban-daban na rayuwa kama daga yan siyasa, yan kasuwa, jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya da kuma masu nishadantarwa.

Lambar yabon wannan shekarar ya hada da GCON biyar, CFR 54, CON 67, OFR 64, OON 101, MFR 75, MON 56 da FRM 8.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng