Fitaccen Gwamnan Najeriya Ya Haramta Ayyukan Kungiyoyin Direbobin Bas Da Adaidaita Sahu A Jiharsa

Fitaccen Gwamnan Najeriya Ya Haramta Ayyukan Kungiyoyin Direbobin Bas Da Adaidaita Sahu A Jiharsa

  • Kungiyar direbobi ta rasa muhalli a jihar Anambra bayan takunkumi da gwamnatin jihar ta kakaba mata
  • An tattaro cewa masu haya da adaidaita sahu, direbobin bas za su rika biyan harajinsu kai tsaye ga gwamnatin jihar suk sati ko mako
  • A bangare guda, an bukaci yan gareji da tashohin mota su yi rajistan sunansu da gwamnatin jihar don koyar da su sana'o'i

Anambra - A wani mataki na Gwamna Charles Soludo na saita jihar Anambra kan turba ta cigaba, an haramta dukkan kungiyoyin masu adaidaita sahu (keke) da motoccin bas yin aiki a jihar.

Jigo a jam'iyyar APC, Joe Igbokwe ne ya sanar da hakan a wani wallafa da ya yi a dandalin sada zumunta a ranar Juma'a 30 ga watan Satumba.

Gwamna Soludo
Soludo Ya Haramta Ayyukan Kungiyoyin Direbobin Bas Da Adaidaita Sahu A Jihar Anambra. Hoto: Charles Soludo.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar wallafar da Legit.ng ta gani, an gabatar da wasu sabbin tsare-tsare bayan haramta kungiyoyin na yan bas da masu adaidaita sahu a jihar.

Wasu daga cikin tsare-tsaren sun hada da wajabtawa direbobin bas, akori-kura, da sauran motoccin daukan kaya biyan harajin N5000 duk sati ko N20000 a wata.

An umurci masu adaidaita sahu su rika biyan N4000 duk sati ko N15000 duk wata.

A bangaren masu tafiya daga jiha zuwa jiha, gwamnatin jihar ta bukaci su rika biyan N6250 duk sati ko N25000 duk wata.

Amma, an tattaro cewa za a bawa direbobin inshora ta lafiya.

Soludo ya gargadi direbobi masu karya doka, ya fadi hukunci

Kazalika, an gargadi direbobi mota da masu adaidaita sahu wadanda suka ki bin dokar su shirya fuskantar fushin hukuma.

Wallafar ta ce:

"Za a hukunta duk wani mutum ko tawaga wacce ta nemi kafa kungiya ko hada kan yan bas ko masu adaidaita sahu."

An tattaro cewa gwamnatin jihar ta shawarci matasa da ke aiki a tashohi da gareji su yi rajista da gwamnati don a koyar da su sana'o'in hannu.

Dukkan Yan Bindigan Da Aka Kama A Anambra Yan Kabilar Ibo Ne, In Ji Gwamna Soludo

A wani rahoton, Chukwuma Soludo, gwamnan Jihar Anambra, ya ce dukkan yan bindigan da aka kama a jihar kawo yanzu yan asalin yankin kudu maso gabas ne, The Cable ta rahoto.

Soludo, ya bayyana hakan ne lokacin da aka yi hira da shi a shirin Sunday Politics, a gidan talabijin na Channels TV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel