'Yan Bindiga Sun Karbi Mudu 20 Na Shinkafa, 20 Na Wake a Matsayi Kudin Fansa, Sun Saki Mutum 12

'Yan Bindiga Sun Karbi Mudu 20 Na Shinkafa, 20 Na Wake a Matsayi Kudin Fansa, Sun Saki Mutum 12

  • Tsagerun 'yan bindiga sun sako mutane 12 bayan karbar mudannin kayan abinci a jihar Kaduna ta Arewa maso Yamma
  • An sace akalla mutane 20 a wani yankin jihar, ana neman kudin fansa Naira miliyan 12 daga hannun iyalai
  • An kashe manomi bayan daure shi a jikin bishiya, kana wasu mutanen da aka sace sun tsere daga hannun 'yan bindiga

Jihar Kaduna - 'Yan bindiga a Birnin Gwani ta jihar Kaduna sun sako wasu mutane 12 bayan karbar mudu 20 na shinkafa, 20 na wake, jarkar manja, man gyada da katin waya na N10,000 a matsayin fansa, The Nation ta ruwaito.

Amma an ruwaito cewa, 'yan bindigan sun hallaka wani manoma tare da yin awon gaba da mutane 20 daga gonakinsu a yankin Jangali da Kwaga duk dai a yankin Birnin Gwani.

Kara karanta wannan

An gano wata maboyar 'yan bindiga a Arewa, an fatattaki tsageru, an ceto mutanen da aka sace

Kungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari (BEPU) ce ta fitar da sanarwar hakan ta hannun shugabanta, Ishaq Usman Kasai a jiya Alhamis 29 ga watan Satumba.

Yadda 'yan bindiga suka karbi abinci a matsayin fansan mutum 12
'Yan Bindiga Sun Karbi Mudu 20 Na Shinkafa, 20 Na Wake a Matsayi Kudin Fansa, Sun Saki Mutum 12 | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa, 'yan bindigan sun nemi Naira miliyan 12 a matsyain kudin fansa daga wasu manoman da suka sace, rahoton jaridar Leadership.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar sanarwar:

"An sako mutum hudu da aka sace a Unguwar Liman da kuma daya da aka sace a unguwar shekarau a jiya Laraba bayan biyan miliyan 2 da N500,000 bi da bi."
"Manoma biyar da aka sace a ranar Alhamis 15/9/2022 a Kurgin Gabas da Sabin Layi sun yi nasarar kubuta daga maboyar 'yan bindiga bayan shafe mako guda a can.
"Abin bakin ciki, an kashe wani manomi a yankin Shiwaka ranan Talata 27/9/2022 bayan daure shi a jikin bishiya; kuma sama da mutum 20 aka sace a ranar Laraba 28/9/2022."

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

Sojin Sama Sun Sake Ruwan Bama-Bamai Kan Maboyar ’Yan Bindiga a Zamfara

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, rundunar sojin saman Najeriya ta sake gano mafakar 'yan ta'adda karkashin jagorancin Dan Karami a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Jaridar Punch ta ce, sojojin sun yi nasarar jefa bama-bamai kan mafakar 'yan bindigan da ke addabar jama'ar yankin.

A cewar wata majiyoyi daga yankin, an kashe wasu 'yan bindiga da dama a harin da aka kai jiya Alhamis 22 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel