Kishiya Da Dangin Miji Ne Suka Saka Ni Gaba Da Gori, Matar Da Ta Sace Jinjiri Daga Asibiti

Kishiya Da Dangin Miji Ne Suka Saka Ni Gaba Da Gori, Matar Da Ta Sace Jinjiri Daga Asibiti

  • Jami’an tsaron farin kaya na DSS sun damke matar da ta sace jaririn kwana takwas daga asibitin ATBUTH a Bauchi
  • Matar ta bayyana cewa ta sace jaririn ne saboda kishiyarta da dangin miji sun saka ta gaba da titin haihuwa
  • An gano matar ne bayan ta je gida da jaririn inda ta sanar da cewa ta haife shi ne amma mijinta bai yarda ba

Bauchi - Jami’an tsaron farin kaya sun dam ke wata mata kan zarginta da sace jaririn kwana takwas mai suna Ibrahim Mohammed daga asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi.

Yaron da aka samo daga wacce ake zargin an mika shi ga iyalansa a ranar Talata, jaridar Punch ta rahoto.

Uwa da jariranta a Bauchi
Kishiya Da Dangin Miji Ne Suka Saka Ni Gaba Da Gori, Matar Da Ta Sace Jinjiri Daga Asibiti. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

Wacce ake zargin ta yi basaja a matsayin ma’aikaciyar jinya sannan ta aikata laifin.

Kamar yadda majiyar tace, wacce ake zargin ta sace jinjirin ne saboda yadda kishiyarta da dangin mijinta ke mata gori saboda rashin haihuwa.

An tattaro cewa wanda ake zargin ta kai jaririn gidanta dake kauyen Dull a karamar hukumar Tafawa Balewa inda tace ta haihu.

Mijnta bai amince bai inda ya musanta cewa ba ‘dan ta bane.

Daga bisani mijin ya gano cewa an sace jariri daga ATBUTH, kishiyarta ta bayyana kuma aka kai lamarin wurin jami’an tsaro.

Wata majiya ta ce:

“Bayan samun bayanin, jami’an DSS sun ziyarci yankin kuma suka samo jaririrn da matar wacce a take aka kama ta. A yanzu tana hannu jami’an DSS don bincike.
“A bayaninta, an gano cewa wacce ake zargin bata taba haihuwa ba. Ta ce ta sace jaririn saboda zundenta da kishiya da ‘yan uwan mijinta ke mata.”

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki shida, An Ceto Jaririn Da Wata Mata Ta Sace A Asibitin ATBU Bauchi

Mahaifiyar jaririn mai suna Bilkisu Alhassan, ta bayyana wacce ake zargin ta zo tare da sanar mata cewa jaririn na bukatar madara da wasu sinadarai.

Ta ce:

“Na sanar mata cewa mahaifinsa ya siyo abincin yara amma ba wacce suke bukata bace amma wani daban.
“Ta tambaye ni wanne daga cikin jariran ne babba kuma na nuna mata Ibrahim. Daga nan ta dauke shi tayi gaba. Ta sanar dani cewa za ta kai shi sashin yara.
“Ban san ta ba amma na yarda da ita. Nace ta jira sirikata ta dawo, amma ta yi gaba da shi.”

A zantawar da Legit.ng Hausa tayi da wani likita ma'aikacin asibitin ATBUTH da ya bukaci a boye sunansa saboda ba shi ne a matsayin zantawa da manema labarai ba, ya bayyana cewa wannan babban abun tada hankali ne.

Duk da ya tabbatar da cewa an ceto jaririn, yace mahaifiyarsa ta matukar ba shi tausayi lokacin da ya ga halin da ta shiga bayan batan jaririnta duk kuwa da tagwaye ne ta haifa.

Kara karanta wannan

"Ba Kuskure Bane" Jam'iyyar APC Ta Faɗi Dalilin Sanya Jigon PDP a Kamfen Tinubu, Ta Maida Martani Ga Gwamnoni

Yace a halin yanzu ana shirin gyara tsaron tsaro na asibitin kuma hakan ba za ta sake faruwa ba da kowa da izinin Allah.

Jami’an Tsaro Sun Ceto Jariri ‘Dan Wata 13 Daga Hannun Masu Garkuwa da Mutane

A wani rahoton, Jami’an ‘yan sandan reshen jihar Edo sun yi nasarar hallaka wasu miyagu a cikin gungun mutane shida da ke yin garkuwa da Bayin Allah.

Tribune ta fitar da rahoto a yau ranar Laraba, 14 ga watan Satumba 2022 cewa ‘yan sanda sun kashe ‘yan bindiga uku a kan titin Benin zuwa Auchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel