Dalar Amurka Ta Kara Birkicewa a Kasuwa Yayin da Aka Fara Kamfe a Najeriya
- Dalar Amurkar da aka saida N718 ko N720 a makon da ya gabata, ta zama N735 a yammacin Laraba
- Sai da ‘Yan canji suka saye Dala 1 a kan N728, suka saida ta a N735 a Bureau De Change a jiyan nan
- A makon nan aka soma yakin neman zaben shugaban kasa, wannan bai rasa alaka da farashin
Abuja – Har zuwa yanzu, tattalin arzikin Najeriya yana cigaba da fuskantar kalubale ta fuskar sukurkucewar darajar Naira a kasuwa.
Wani rahoto da muka samu daga Punch, ya tabbatar da cewa darajar Naira ya kara yin kasa a kan Dala a ‘yan makonnin bayan nan.
Kamar yadda muka ji, a ranar Laraba, 28 ga watan Satumba 2022, abin da aka saida kowace $1 a wasu kasuwannin canjin ya kai N735.
‘Yan canji na Bureau De Change da ke garuruwan Legas da Abuja sun saida Dalar Amurka ne tsakanin N718 zuwa N720 a makon jiya.
N718 zuwa N735 a kwana 7
Yanzu haka maganar da ake yi, farashin Dala yana yawo tsakanin N728 zuwa N735. Kusan an samu karin N10 zuwa N15 a mako daya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bala Usman ‘dan canji ne a kasuwar Amuwo-Odofin da ke Legas, ya shaidawa jaridar cewa ba a saida Dalar Amurka ($1) a kasa da N728.
“N728 ne, ba za a iya saida ta kasa da haka ba.”
- Bala Usman
Wani takwaransa, Abubakar Jamiu da ke Zone 4 a birnin tarayya Abuja ya nuna cewa farashin da ake samun Dala a Legas ya ma yi araha.
“Dala tayi tsada, a N730 muke saida ta, babu kari-babu ragi.”
- Abubakar Jamiu
Farashi ya kara tashi da yamma
Rahoton yace zuwa yammacin jiya, sai da farashin $1 ya kai N735, har a Legas an saida kowace Dala a farashin kafin a rufe kasuwa.
Da kimanin karfe 5:00 na jiya, wani ‘dan canji da ke Lagos Island yace zai saye Dala a kan N728, sai ya saidawa masu nema a kan N735.
Har farkon makon nan, a banki dai abin da ake saida Dalar ba ta wuce N430. Masana suna ta’allaka karyewar Nairar da tsare-tsaren tattali.
An rasa N160 a kwanaki 360
A Satumban 2021, shekara daya kenan, aka ji labari ‘Yan canji suna saida Dalar Amurka a kan sama da N570 a irinsu Legas da Kano.
Idan za a tuna, a kasuwannin BDC na Kano, farashin Dala ya kai N575. Jama'a sun rika sayen Pound Sterling, £1 a kan N780 ne a lokacin.
Asali: Legit.ng