Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Litinin a Matsayin Hutun Ranar ’Yancin Kai
- Gwamnatin tarayya ta ware ranar Litinin a matsayin ranar da ma'aikata za su huta a Najeriya a bikin 'yancin kai
- Najeriya ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960
- A ranar Asabar mai zuwa ne 'yan Najeriya za su yi murnar kubuta daga mulkin turawan mallaka
Gwamnatin Najeriya ta ware ranar Litinin, 3 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutun ma'aikata a kasar a murnar da ake na ranar samun 'yancin kai.
Ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, The Nation ta ruwaito.
Ya kuma taya 'yan Najeriya murnar zagayowar ranar 'yanci tare yin addu'ar Allah kawo karshen kalubalen da kasar ke fuskanta.
A sanarwar da ministan ya fitar, ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Duniya na fuskantar kalubalen tattalin arziki da na tsaro wanda kuma ya shafi kasarmu. Sai dai, ina mai tabbatar muku cewa gwamnati ba za ta watsar da mutane ba, za ta ci gaba da tunkarar wadannan kalubale da dukkan ikonta har sai an samu mafita."
Sanawar da sakataren dindindin na ma'aikatar, dr Shuaib Belgore ya fitar ta bayyana halin da Najeriya ke ciki, rahoton Vanguard.
Ya kuma bayyana cewa, Najeriya za ta samu ci gaba da abubuwa masu kyau a nan gaba kadan.
A rana irinta Litinin mai zuwa ne Najeriya ta kubuta daga hannun turawan mulkin mallaka, inda suka samu 'yanci tare da kafa gwamnati da 'yan kasar ke gudarwa.
Ya zuwa yanzu, Najeriya ta kai shekaru 62 da samun 'yancin kai.
Babu Wata Jiha da Aka Ba Izinin Mallakar Makamai Masu Sarrafa Kansu, Martanin Fadar Buhari Ga Gwamna Akeredolu
A wani labarin kuma, gwamnatin Najeriya ta ce, babu wata jiha a Najeriya da ke da ikon mallakar makamai masu sarrafa kansu kamar dai bindigogi kirar AK47, TheCable ta ruwaito.
Wannan batu na fitowa ne daga wata sanarwa da fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fitar a yau Talata 27 ga watan Satumba.
Gwamnati ta ce, mallakar bindiga kirar AK47 matukar ba a hannun jami'an tsaro bane to tabbas ya saba doka, kuma akwai hukunci a kai.
Asali: Legit.ng