Tashi Ka Nemi Abun Yi: Fusatattar Matar Aure Ta Dangwararwa Da Miji Kwano Babu Abinci
- Wata mata ta ja hankali sosai a TikTok bayan ta gabatarwa mijinta da kwano babu abinci a ciki a wani bidiyo da ya yadu
- Ta dangwaran masa da rufaffen kwanon a kan teburin gabansa sannan ta bukaci da ya fita ya nemi aiki, tana mai cewa bai san komai ba sai ci
- Masu amfani da TikTok da dama sun sanya baki cikin lamarin yayin da suka bayyana ra'ayoyinsu
Masu amfani da TikTok sun yi martani ga wani bidiyo na wata mata da ta gabatarwa mijinta kwano wayam babu abinci a ciki.
A cikin bidiyon, mutumin ya zauna yana jiran a kawo masa abincinsa, kawai sai gashi an dangwaran masa da kwano babu komai.
A cewar matar, mutumin bai da wani aiki sai na tambayar abinci ba tare da fita aiki ko kawo gudunmawar komai ba.
Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Aka Yi Mata Kwalkwabo Bayan Mutuwar Mijinta, Bidiyon Ya Taba Zukata
Ta bukaci mutumin da ya je ya nemi aiki don ya fara kawo nasa gudunmawar. Mutumin ya kadu da abun da matar tasa tayi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Koda dai bidiyon ya yi kama da zolaya, mijin ya ci fuska kuma hakan ya janyo martani. Ga wasu daga cikin martanin a kasa:
@user6042534519611 ya ce:
"Kara yaji dan Allah."
@tracyannandem ta yi martani:
"Malami ki ba mutumin cokali mai yatsu kuma ina nikakken timatir da yaji."
@rose_pro6 ta ce:
"Kwarai kwarai idan namiji baya aiki baya cin abinci."
@Candy ta yi martani:
"Bani da matsala da miji mara aiki ina dai da matsala da mijin da ke jin dadin rashin aikin."
@Vera Tull ta ce:
"Yayi maki kyau yarinya, yana da waya amma bai da aikin yi."
Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Aka Yi Mata Kwalkwabo Bayan Mutuwar Mijinta, Bidiyon Ya Taba Zukata
A wani labarin, wata matashiya yar Najeriya mai shekaru 23, ta yi alhinin rashin mijinta a shafin soshiyal midiya bayan ya yi mutuwar faran daya.
An gano matashiyar wacce ke juyayi a cikin wani bidiyon TikTok a yanayi na alhini da hawaye a idanunta yayin da wasu taron mata ke aske mata gashin kanta.
Ta koka cewa abun akwai ciwo sosai yadda ya zama bazawara a karancin shekaru irin nata. Ta tambayi dalilin da yasa mutumin bai tsaya ba bayan sun shirya yadda rayuwarsu Za ta kasance.
Asali: Legit.ng