Magani a gonar yaro: Amfanin kubewa 5 ga jikin dan adam da baku sani ba
Kubewa dai wata shuka ce da ake anfani da ita musamman ma dai a kasar Hausa wajen yin miya kuma ana shuka ta ne mafi yawanci a kasar Hausa.
Akan yi anfani da ita a danyar ta kokuma idan an busar da ita domin yin miyar da za'a rika cin tuwo.
Legit.ng ta binciko daga majiyar mu wasu anfununnikan ta da dama domin anfanin mu gaba daya.
1. Kubewa tana da sinadarin karin gani na Vitamin A a turance wanda yake da matukar tasiri wajen kara karfin idon dan adam.
2. Kubewa tana kara lafiyar ciki musamman ma ga masu amosanin ciki da kuma dankanoma.
3. Kubewa tana dauke da sinadarin dake kara laushi da kuma lafiyar fatar jikin dan adam.
4. Kubewa tana dauke da sinadarin Vitamin C
5. Kubewa tana daidaita gudun jini
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng