Rashin Wutar Lantarki Ya Tirsasawa Majalisar Tarayya Dage Zamanta
- Rashin wutar lantarki a zauren majalisar wakilan Najeriya ta tirsasa su tashi daga zaman da suke tare da dage shi
- Ana tsaka da zaman majalisar ne ma'adanar wutar lantarkin majalisar ta dinga daukewa har sau biyu
- Tuni kakakin majalisar ya roki sauran 'yan majalisar su dage zaman, duk da kafin ya gama magana sun fada cikin duhu
FCT, Abuja - Rashin wutar lantarki a sabon ginin da 'yan majalisar wakilai ke gudanar da zaman majalisar bayan aikin gyaran da ake yi a zauren majalisar ya tilastawa majalisar dage zaman ta na ba zato ba tsammani a ranar Talata.
Majalisar ta kammala karatu na biyu a kan kudirin yin gyara ga Dokar Shaida, Cap. E14, Dokokin Tarayyar Najeriya, 2004 don kawo tanade-tanaden da suka yi daidai da Ci gaban Fasaha ta Duniya a cikin Shaida yayin da wutar lantarki ta dauke a karo na biyu.
Yayin da yake tambayar ‘yan majalisar ko ya kamata majalisar ta dage zaman sakamakon rashin wutar lantarkin, shugaban majalisar ya ce:
“Masu girma ‘yan majalisa, shin za mu iya dage zaman majalisar kafin a tashi taron saboda kada ma'adanar wutar lantarkin ya mutu?"
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tuni UPs din ya mutu kafin shugaban majalisar ya karasa magana, lamarin da ya jefa zauren cikin duhu, jaridar The Nation ta rahoto.
A wani bangare kuwa, majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta bayar da taimako ga iyalan malamin Yobe, Sheikh Goni Aisami, wanda ake zargin wani soja mai suna John Gabriel ya halaka a watan Agusta a karamar hukumar Karasuwa, lamarin da ke gaban kotu yanzu.
Da yake amincewa da kudirin da Zakariyya Galadima ya gabatar a gaban majalisar, 'yan majalisar wakilan sun yanke shawarar neman gwamnatin tarayya ta taimaka wa dangin ta hannun rundunar sojojin Najeriya har sai an kammala shari’ar.
Gwamnatin Tarayya Ta Ciyo Bashin N1tr Don Biyan Kudin Tallafin Man Fetur Bana
A wani labari na daban, Gwamnatin tarayya ta karbi bashin N1 trillion domin biyan kudin tallafin man fetur a shekarar nan, Dirakta Janar na ofishin manejin basussuka DMO ta bayyana.
Dirakta Janar, Ms. Patience Oniha, ta bayyana hakan yayin gabatar da lakca kan yin kasafin kudi a Army Resource Centre, dake Abuja, rahoton TheNation.
Oniha tace rashin kudi ne ya tilastawa gwamnati kara cin bashin N1trillion don iya biyan kudin tallafin mai.
Asali: Legit.ng