Majalisar Dattawa Ta Nemi Buhari Ya Tsige Gwamnan CBN Daga Wani Babban Mukami

Majalisar Dattawa Ta Nemi Buhari Ya Tsige Gwamnan CBN Daga Wani Babban Mukami

  • Kudirin da ke neman a rage karfin gwamnan babban bankin CBN ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa
  • Yan majalisa na son wani da ba gwamnan babban bankin kasar ba ya zama shugaban hukumar CBN
  • Majalisar na kuma so a janye ikon hukumar na tabbatarwa da kayyade albashi da alawus din mambobinta da amincewa da kasafin kudin bankin na shekara

Abuja - A ranar Talata ne kudurin neman rage karfin ikon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa, Daily Trust ta rahoto.

Kudirin wanda Sanata Sadiq Umar ya dauki nauyinsa, ya nemi a yiwa dokar CBN mai lamba ta 7 gyara domin bayar da damar nada wani daban wanda ba gwamnan babban bankin ba a matsayin shugaban hukumar gudanarwar bankin.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023

Gwamnan CBN
Majalisar Dattawa Ta Nemi Buhari Ya Tsige Gwamnan CBN Daga Wani Babban Mukami Hoto: Capital Post
Asali: Twitter

A dokar CBN na yanzu, gwamna mai ci aka nada don zama shugaban hukumar gudanarwar babban bankin.

Sauran mambobin hukumar sune mataimakan gwamnan hudu, sakataren dindindin, ma’aikatar kudi, dakaraktoci biyar da babban akanta janar na tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ke da alhakin tsarawa da gudanar da gaba daya harkoki da kasuwancin bankin, ciki harda tsarawa da aiwatar da manufofin chanjin kudi dama la’akari da amincewa da kasafin kudin bankin na shekara.

A cikin kudirin, majalisar dattawan ta kuma bukaci a janye ikon hukumar CBN na tabbatarwa da kuma kayyade albashi da alawus din mambobinta da kuma dubawa da amincewa da kasafin kudin bankin na shekara.

Sanata Umar, da yake jawabinsa a muhawarar, ya ce manyan bankunan kasa a duniya suna da mutane na daban a matsayin babban shugaba da kuma shugaban hukumar gudanarwa.

Da take goyon bayan kudirin, Sanata Betty Apiafi ta ce gyaran ya zama dole duba ga yadda aka dunga daukar gwamnan mai ci, Godwin Emefiele, a matsayin dan takarar shugaban jasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Mayun shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Wasu Manyan Gwamnonin Arewa 3 Na Shirin Marawa Peter Obi Baya

Ta ce:

“Gwamnan na CBN ya kauce hanyarsa don takarar shugaban kasa yayin da yake mulki a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa a 2022.
“Wannan ba zai taba faruwa ba a koina a duniya, duba ga cewa ana sa ran za a ajiye kayayyakin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a bankin.
“Kasancewar Godwin Emefiele ya yi yunkurin takarar shugabancin kasar yasa yan Najeriya sun yanke kauna da bankin wajen ajiye kayan INEC.”

Shugaban majalisar dattawan, Ahmad Lawan, ya gargadi sanatocin da su mayar da hankali kan bukatar gyaran maimakon karkata zuwa ga yunkurin gwamnan CBN din nayin takara tunda gaba daya baya cikin manufofin kudirin.

Bayan tsallake karatu na biyu, an tura kudirin zuwa ga kwamitin banki, inshore da sauran hada-hadar kudi don yin aiki a kai.

Zaben 2023: Shugaba Buhari ya bayyana yadda sabbin shugabannin za su samu

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna yakinin cewa gwamnatinsa za ta gudanar da tsarin mika mulki mai kyau inda sabbin shugabannin siyasa zasu bayyana.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

Shugaban kasar ya yi jawabi ne a ranar Talata yayin da ya karbi wasiku daga jakadu da manyan kwamishinonin kasashe shida a fadar shugaban kasa, Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Jakadu da manyan kwanishinonin sun hada da na Indiya, Mista Gangadharan Balasubramanian, Jamus, Annett Gunther, Sudan, Mohamed Yousif Ibrahim Abdelmannan, Damocradiyar Kongo, Misis Gerengbo Yakivu Pascaline.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng