A Garkame Coci a Jihar Kogi, Inda Fasto Ke Ba da Ruwa da Sunan Maganin Bindiga
- Gwamnatin jihar Kogi ta garkame wani cocin da ya bude wani irin asibiti da ba a saba ganin irinsa ba
- An kame wani faston da ke ba da maganin bindiga a cocinsa, ya kuma bude wurin karbar haihuwa ba tare da izinin gwamnati ba
- Hukumomi sun ce, abubuwan da ake a cocin ya saba doka, don haka ana kokarin yadda za a gurfanar da faston a kotu
Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya umarci a garkame wani coci mai hade da asibiti mai suna New Jerusalem Deliverance Ministry da ke Okene bisa zargin fasto na damfarar mabiyansa.
Rahoton da muka samo daga jaridar Punch ya ce, ana zargin cocin da ba mabiyansa wani ruwa da ake tunanin marasa tsafta ne da sunan maganin bindiga.
Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda Da Wasu 3, Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Masu Yawan Gaske A Jihohin Arewa 2
Faston cocin, Peter Adeiza ya ce yana gudanar da cocin tun 2008, kuma an ce mutane da dama sun mutu sakamakon rashin tsaftar ruwan da ake basu.
Mashawarcin gwamnan jihar kan harkokin tsaro, kwamanda Jerry Omodara (mai ritaya) ne da sauran jiga-jigan gwamnatin jihar suka garkame cocin a jiya Litinin 26 ga watan Satumba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano cewa, baya ga kebe wani asibiti da ake karbar haihuwa da warkar da maras lafiya a hade da cocin, ana kuma jinyar masu tabin hankali a cocin.
Akwai hujjoji a kan faston
Mambobin cocin sun bayyana cewa, suna yawan karbar magunguna daga babban malamin nasu da suka kira 'Man of God'.
Jaridar Daily Post ta tattaro yadda wasu da suka yi jinya a asibitin da ke karkashin cocin suka bayyana irin wahalar da suka sha.
Hadimin gwamnan ya kuma bayyana cewa, a baya an kame faston bayan samun bayanan sirri gamr ayyukan da yake yi.
Omodara ya kuma kara da cewa, akwai isassun hujjoji da ke tabbatar da abin da faston ke yi ya saba addini, kuma ya saba da koyarwar harkar kiwon lafiya.
Hakazalika, ya ce za a gurfanar da faston nan ba da dadewa ba a gaban kotu.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Edward Egbuka, da ya samu wakilicin kwamandan yanki, ACP Ibrahim Usman ya ce, jami'an tsaro na ci gaba da sa ido a harabar cocin don tabbatar da doka da oda.
Sojin Sama Sun Sake Ruwan Bama-Bamai Kan Maboyar ’Yan Bindiga a Zamfara
A wani labarin, rahoton da muke samu ya bayyana cewa, rundunar sojin saman Najeriya ta sake gano mafakar 'yan ta'adda karkashin jagorancin Dan Karami a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Jaridar Punch ta ce, sojojin sun yi nasarar jefa bama-bamai kan mafakar 'yan bindigan da ke addabar jama'ar yankin.
A cewar wata majiyoyi daga yankin, an kashe wasu 'yan bindiga da dama a harin da aka kai jiya Alhamis 22 ga watan Satumba.
Rashin Tausayi: Wani Dalibin Najeriya Ya Halaka Mahaifinsa Da Mahaifiyarsa, Ya Rufe Gawarsu A Daki Ya Tsere
Asali: Legit.ng