Babban Malamin Addinin Musulunci Yusuf Al-Qardawi Ya Rasu

Babban Malamin Addinin Musulunci Yusuf Al-Qardawi Ya Rasu

  • A ranar Litinin ne aka samu labarin rasuwar babban malamin addinin Islama a duniya, Sheikh Yusuf Al-Qardawi
  • Majiyoyi basu bayyana silar rasuwarsa ba, amma ana kyautata zaton ya rasu ne a kasa Qasar a yankin Labarabawa
  • Al-Qardawi na daya daga cikin malaman da ake yawan cece-kuce a kansu a duniyar ilimi a fadin duniya

Qatar - Malamin addinin Islaman nan, fitacce a duniya, Sheikh Yusuf Al-Qardawi ya riga mu gidan gaskiya, AlJazeera ta ruwaito.

Malamin dan kasar Masar da ke da zama a kasar Qatar ya kasance shugaban kungiyar hadin kan malaman addinin muslunci ta kasa da kasa, kuma shine mu'assasin tafiyar Ikhwan.

An sanar da rasuwar malamin ne a shafinsa na Twitter a yau Litinin 26 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

2023: Rawar Da Nake Takawa Na Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a Sirrince, Saraki Ya Magantu

Sheikh Yusuf Al-Qardawi ya rasu
Babban malamin addinin Musulunci Yusuf al-Qaradawi ya rasu | Hoto: aljazeera.com
Asali: UGC

Kadan daga tarihinsa

Al-Qardawi sananne ne sosai a tashar talabijin na AlJazeera, inda yake gabatar da shiri a harshen labarci kan maudu'in ilimin 'Shari'a da Rayuwa'.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kasance daya daga cikin malaman da ake yawan cece-kuce akansu tun bayan da aka hambarar da mulkin shugaban Masar Mohamed Morsi a 2013, shugaban mulkin dimokradiyya.

Morsi dai babban mamba tafiyar Ikhwan wacce Al-Qardawi ya assasa, kuma ma'abota tafiyar sun yi tasiri wajen kawo gwamnatin Morsi.

Al-Qardawi bai sake dawowa Masar ba tun bayan hambarar da mulkin Morsi saboda yadda yake adawa da gwamnatin shugaba Abdel Fattah el-Sisi.

A baya can, an taba korar malamin daga Masar kafin 2011, lokacin da aka hambarar da gwamnatin shugaba Hosni Mubarak.

Rasuwarsa ta jawo cece-kuce a duniyar Musulmai, kuma mutane da dama sun yi jimami a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Bayyana Abinda Zai wa 'Yan Najeriya 100m a Fannin Lafiya Idan Ya ci Zabe

Labaarin Wani Dan Saudiyya Ya Yi Ikirarin Cewa Ya Yi Aure Sau 53 a Cikin Shekaru 43

A wani labarin, a kokarinsa na neman kwanciyar hankali da dadin rai, wani balarabe ya fadi tarihin rayuwarsa, ya ce mata 53 ya aura a cikin shekaru 43 kacal.

Abu Abdullah ya ce ya yi aurensa na farko ne a lokacin yana da shekaru 20, kuma matar da ya aura ta girme shi da shekaru shida.

An kakaba masa “Polygamist of the century”, wato mutumin da ya fi yawan aure-aure a wannan kanin saboda yawan auren da ya yi, kamar yadda MBC ta bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel