Sojojin Najeriya Sun Kai Samame Kan 'Yan Ta'adda da Manyan Makamai a Yobe

Sojojin Najeriya Sun Kai Samame Kan 'Yan Ta'adda da Manyan Makamai a Yobe

  • Dakarun sojin Najeriya sun harba makamai masu haɗari kan mayaƙan kungiyar ISWAP bayan samun bayanan sirri a Yobe
  • Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa tulin 'yan ta'addan sun rasa rayukansu sakamakon samamen sojin
  • Haka nan, wasu mayaƙan ISWAP sun kashe ɗan Banga tare da jikkata wasu hudu a harin tsakar dare a jihar Borno

Yobe - Wasu manyan makamai da rundunar sojin Najeriya suka harba sun tashi da mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ISWAP, da yawansu sun sheƙa barzahu a jihar Yobe.

Rahoton Leadership ya nuna cewa tawagar 'yan ta'addan sun taru a wani wuri da ake kira Wulle a kan Babura da Motoci da nufin kai hari wani sansanin Soji mafi kusa.

Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya Sun Kai Samame Kan 'Yan Ta'adda da Manyan Makamai a Yobe Hoto: leadership
Asali: Facebook

A wani rahoton sirri da Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi ya samu daga majiyar Soji, ya nuna cewa bayan gano shirinsu, dakarun Bataliya ta 27 suka harba makamai wurin.

Kara karanta wannan

Borno: Zulum Ya Sanar da Abun Mamakin da Ya Faru da 'Yan Ta'adda Wanda Ba a Taba ba a Duniya

A cewar rahoton, sakamakon harba manyan makaman, 'yan ta'adda da yawa waɗanda suka taru a wurin suka rasa rayukansu, har yanzu ba'a gano adadin da aka kashe ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayanai sun ce bayan faruwar haka, wasu 'yan ta'adda suka koma wurin da Babura Shida da Mota ɗaya domin kwashe gawarwarkin 'ƴan uwansu.

Yan ta'dda sun kashe Ɗan Banga a Borno

A wani cigaban kuma, mamban ƙungiyar yan banga (CJTF) ya rasa rayuwarsa yayin da wasu huɗu suka jikkata a wani farmakin tsakar dare da mayaƙan ISWAP suka kai kauyen Benisheik.

Ƙauyen wanda ke ƙaramar hukumar Kaga na da nisan Kilomita 72 da mil 44.8 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Rahoto ya bayyana cewa yan ta'addan sun shiga kauyen da ƙarfe 3:30 na dare, suka yi kazamar musayar wuta da jami'an tsaron, suka kashe ɗaya suka jikkata huɗu.

Kara karanta wannan

"Ba Kuskure Bane" Jam'iyyar APC Ta Faɗi Dalilin Sanya Jigon PDP a Kamfen Tinubu, Ta Maida Martani Ga Gwamnoni

Wata majiya tace maharan sun janye kana suka fara gudun neman tsira yayin da suka ga ƙarin dakarun soji sun kai ɗauki.

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari Kan Bayin Allah, Sun Kashe Rayuka a jihar Zamfara

Miyagun 'yan bindiga sun kai sabon mummunan hari kan bayin Allah a garin Tauji dake karamar hukumar Maru a Zamfara.

Bayanai sun yi nuni cewa mutum uku sun rasa rayuwarsu yayin da maharan suka sace mata masu shayarwa guda Takwas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262