Yadda Yan Bindiga Suka Tafi Shagon Wani Dan Kasuwa A Kano Suka Bindige Shi Har Lahira
- Yan bindiga sun tafi har shago sun bindige wani dan kasuwa mai suna Mr Ifeanyi a Sabon Garin Jihar Kano
- Shaidun gani da ido sun bayyana yadda maharan suka taho a mota suka tsallaka titi suka nufi shagon Ifeanyi
- Maharan sun fara harbin abokin Ifeanyi sannan suka bi shi a lokacin da ya yi yunkurin tserewa suka bindige shi har lahira
Kano - Yan bindiga sun harbe wai dan kasuwa, Mr Ifeanyi, har lahira sun kuma raunata abokinsa a wurin sana'arsa a sabon garin Zaria a Jihar Kano.
Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar a Azubros Plaza, France Road, Sabon Garin Kano.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shaidun gani da ido sun magantu
Shaidu sun ce babu wanda ya san inda yan bindigan suka fito ba har sai da suka ji karar harbin bindiga, suka ce maharan sun bindige mutumin sannan suka tsere a motarsu.
Wani shaida wanda ya nemi a sakayya sunansa ya ce:
"Sun zo ne musamman don su kashe Ifeanyi bisa fahimtar mu. Sun tsallako daga titi suka tafi shagonsa. Abokinsa suka fara harbi lokacin da Ifeanyi ya tsere daga shagonsa sai suka bi shi suka bindige shi har lahira.
"Ba su taba kowa ba kuma abin ya daure mana kai. Wurin ya hargitse. Amma bayan sun tafi, komai ya koma daidai sai dai cinkoson motocci."
Wani shaidan gani da idon, Jibrin Usman ya ce an garzaya da abokin marigayin da aka harba zuwa asibiti yana samun sauki.
Duk da cewa kawo yanzu ba a san dalilin kashe shi ba, Daily Trust ta gano cewa marigayin fitaccen dan kasuwa ne da ke sayar da batiri a kasuwan Sabon Gari.
Kawo yanzu yan sanda ba su ce komai kan lamarin ba.
Wakilin Legit.ng Hausa ya samu ji ta bakin wata mata, Grace, da ke zaune a Sabon Garin Kano inda ta yi karin haske.
Ta ce ta samu bayani a unguwa inda wasu ke cewa a Niger road abin ya faru wasu kuma suka ce a France, amma abinda dukkansu suka yi tarayya a kai shine kan babura maharan suka taho.
Grace ta cigaba da cewa:
"Abin ya faru ne tsakanin karfe 9 zuwa 10 na dare.
"Sun taho a kan babura ne suka tsallaka titi suka nufi shagon mutumin kai tsaye suka harbi abokinsa kafin shima suka harbe shi har sai da ya ce ga garin ku".
Ta kara cewa a dukkan bayyanan da ta samu a unguwar babu wanda ya bayyana irin tufafin da suka ce.
Ta ce:
"Ka san idan irin wannan abin ya faru hankulan mutane tashi ya ke yi kawai tsira suke nema. Ba a cika kai hankali a lura da abin da tufafin da maharan ke sanye da shi ba."
Yan Ta'adda Sun Sake Kai Hari Masallacin Juma'a a Zamfara, Sun Kashe Masallata Da Yawa
A wani rahoton, yan bindiga sun kai hari masallacin Juma'a da ke garin Ruwan Jema a karamar hukumar Bukkuyum na Jihar Zamfara suka kashe mutane 15, Nigerian Tribune ta rahoto.
Harin na baya-bayan nan ya faru ne makonni uku bayan yan ta'adda a ranar Juma'a sun kai hari a masallaci a garin Zugu a karamar hukumar inda suka kashe mutum 45.
Wani mazaunin garin, Ahmed Bukkuyum ya ce yan bindigan sun boye AK 47 dinsu cikin tufafinsu suka yi kamar sun taho yin sallah ne.
Asali: Legit.ng