Yanzu Fa Ta Karewa Atiku, Jam'iyyarsa Ta PDP Ta Kidime Da Rabuwar Kai: APC

Yanzu Fa Ta Karewa Atiku, Jam'iyyarsa Ta PDP Ta Kidime Da Rabuwar Kai: APC

  • Jam'iyyar APC ta bayyana cewa Alhaji Atiku Abubakar na PDP fa yanzu ya zama abin tausayi
  • APC ta yiwa Atiku Isgili da cewa shi da ke ikirarin hada kan yan Najeriya ya fara da na gidansa PDP
  • Jam'iyyar PDP ta rabu gida biyu tsakanin bangaren Atiku Abubakar da Gwamnan Rivers Nyesom Wike

Kwamitin yakin neman zaben Tinubu-Shettima ya siffanta dan takara shugaban kasa PDP, Atiku Abubakar, a matsayin jagoran mai raba kan mutane.

Jam'iyyar PDP ta shiga rikici biyo bayan zaben fidda gwanin jam'iyyar da akayi a Abuja.

A ranar Juma'a, dirakta yada labaran kwamitin yakin neman zaben APC, Bayo Onanuga, ya ce gaba daya rikicin dake gudana a jam'iyyar PDP na ragewa Atiku karfi.

A cewarsa:

"Ya kamata mu tausayawa Atiku, da alamun takararsa na shugaban kasa za ta bi ruwa. Jam'iyyarsa PDP ta rabe biyu. Abubuwa gaba daya sun tabarbare masa musamman bayan rahoton mujallar The Economist (EIU)."

Kara karanta wannan

Tirkashi: Sunan Sanata PDP, Chimaroke Nnamani Ya Fito Cikin Kwamitin Kamfen APC

"Bayan saba ka'idar kundin tsarin mulkin jam'iyyarsu na kama-kama tsakanin Arewa da Kudu. Atiku ya shiga halin ha'ula'i."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"PDP ta watse, kuma sakamakon haka a bayyana yake Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, na fito-na-fito da Atiku kuma hakan na rage karfin dan takaran shugaban kasa."
"Ikirarin da Atiku yake na cewa shi mai hada kan jama'a ne ya bayyana karara yanzu duk shaci-fadi ne, saboda mambobin jam'iyyarsa kansu ya rabe kuma suna neman adalci."
TInubu
Yanzu Fa Ta Karewa Atiku, Jam'iyyarsa Ta PDP Ta Kidime Da Rabuwar Kai: APC
Asali: Depositphotos

Tinubu Zai Lashe Zaben 2023: Binciken Mujallar Economist (EIU)

Dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaben 2023, cewar Mujallar Economist Intelligence Unit (EIU).

EIU sashen leken asiri da binciken mujallar The Economist ne wanda ke da zama a Landan, kasar Birtaniya wacce ta shahara da hasashe da bincike da take wallafawa wata-wata.

Kara karanta wannan

Wike Ya Jawo Atiku Abubakar Ya yi wa Bola Tinubu Raddi Yayin da Ake Yaki a PDP

Mujallar ta bayana cewa da kamar wuya dan takaran People’s Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar yayi nasara saboda rikici cikin gidan dake faruwa a jam'iyyarsa

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida