Jerin Mutane 3 Da Suka Yi Fice Saboda Halitta Ta Musamman Da Suke Dauke Da Su

Jerin Mutane 3 Da Suka Yi Fice Saboda Halitta Ta Musamman Da Suke Dauke Da Su

  • Allah na halittan mutane iri daban-daban sannan ya sanya masu wasu irin baiwa da kan banbantasu da sauran jama'a
  • Akwai wasu yan gida daya masu dauke da tabon haihuwa, su dukka iyalin suna da wata alama iri guda ta yadda kana ganinsu za ka san akwai alaka ta jini
  • Hakazalika akwai wata karamar yarinya da ita Allah ya halicceta ne dauke da idanu masu launin shudi

A yan baya-bayan nan, an samu wasu yan tsirarun mutane da suka yi fice saboda yanayin halittar da Allah ya yi masu.

Sun fito duniya ta san su ne bayan sun wallafa labaransu a shafukan soshiyal midiya.

Jama’a na shiga mamaki a duk lokacin da suka ji karo da irin wadannan mutane da ba kasafai ake ganin irinsu ba wadanda kan kasance da dabon haihuwa ko kuma wani yanayi na halitta da kan sa su sha banban da sauran mutane.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da bam ya tashi bayan sallar Juma'a, mutane da dama sun mutu

Kananan yara
Jerin Mutane 3 Da Suka Yi Fice Saboda Halitta Ta Musamman Da Suke Dauke Da Su Hoto: TikTok/@gbozimormoses, @alaija.h. and @heyy..cheryl.
Asali: UGC

Su kan zamo abun magana a shafukan intanet saboda da wuya ake cin karo da mutane irinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano irin wadannan mutanen suna shawagi a duniyar intanet. Legit.ng ta gabatar da mutane uku da suka shahara saboda yanayin halittarsu.

1. Budurwa wacce ke da tabon haihuwa irin na kaninta

Wata matashiyar budurwa mai suna @alaija.h. a TikTok ta wallafa wani dan gajeren bidiyo da ke nuna tabon haihuwar da suke dauke da shi daga ita har kaninta.

Tabon mai haske yana kwance ne daga goshi har zuwa bangaren hancinsu.

Yayar tana da irin wannan tabon a tumbinta, ta tabbatar a daya daga cikin bidiyonta cewa wannan tabon a jininsu yake.

2. Uba da ke da wani tabo da farin gashi irin na dansa

Hakazalika, wani mutum mai suna @gbozimormoses a TikTok ya wallafa bidiyonsa tare da dansa yana mai nuna baiwar da Allah ya yi masu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a wata jihar Arewa yayin da 'yan sanda suka kashe matashi dan shekara 16

Wannan tabo na haihuwa ya kasance iri daya sak tsakaninsa da dan nasa kuma hakan ya baiwa mutane mamaki.

Bayan ganin tabon wanda ke goshi da fuskarsu, mutane da dama sun ce ba sai sun yi gwajin ‘ya’yan hallita (DNA) don tabbatar da wanene uban dan ba.

3. Yarinya mai shudin idanu

Wata karamar yarinya ta yi fice a duniyar TikTok bayan mahaifiyarta ta wallafa wani bidiyonta kuma mutane sun lura tana da wani irin launin idanu na musamman.

A cikin bidiyon, mahaifiyar yarinyar ta ce a lokacin da ta lura da idanun yarinyar da aka haifeta, sai taga suna da matukar kyau.

Idanun yarinyar wanda ke kama da na damusa ya burge mutane da dama a soshiyal midiya.

Hotunan Sauyawar Yarinyar Da Aka Haifa A Matsayin Zabiya Shekaru Bayan Mahaifinta Ya Gujeta

A wani labarin, wata uwa da ta cika da alfahari ta nuna yadda kyakkyawar diyarta da aka haifa zabiya ta sauya ta kara kyau.

Kara karanta wannan

Taliban Za Ta Haramta Amfani Da TikTok Saboda Yana 'Asassa Tashin Hankali'

Mahaifiyar yarinyar mai suna Nshai ta ce mahaifin diyar tata ya yi watsi da su lokacin da aka haifi yarinyar. Baya kaunarta saboda an haifeta zabiya.

Sai dai kuma, shekaru bayan nan, yanzu yana roko don ya dawo cikin rayuwarta kuma a matsayin mahaifinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng