Wani Dalibin Najeriya Ya Halaka Mahaifinsa Da Mahaifiyarsa, Ya Rufe Gawarsu A Daki Ya Tsere

Wani Dalibin Najeriya Ya Halaka Mahaifinsa Da Mahaifiyarsa, Ya Rufe Gawarsu A Daki Ya Tsere

  • Ana zargin wani dalibi a jihar Anambra ta kashe mahaifinsa da mahaiyarsa a garin Nnewi na Jihar Anambra
  • Makwabta ne suka gano gawar mutumin da matarsa bayan sun rika jin wari na fitowa daga gidan sannan aka kira hukuma
  • Rundunar yan sanda a Anambra ta tabbatar da afkuwar lamarin ta kuma ce an fara farautar wanda ake zargin da aka ce shine dansu daya kacal

Jihar Anambra - Wani dalibi a makarantun Jihar Anambra da ba a riga an gano shi ba ya halaka mahaifinsa da mahaifiyarsa ya bar gawarsu a cikin daki.

Lamarin ya faru ne a garin Nnewi na Jihar Anambra kamar yadda The Punch ta rahoto.

Taswirar jihar Anambra.
Wani Dalibin Najeriya Ya Halaka Mahaifinsa Da Mahaifiyarsa, Yan Sanda Sun Fara Farautarsa. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

An tattaro cewa gawar wadanda suka rasun ya fara rubewa a lokacin da makwabta suka gano su saboda wari da ke fitowa daga dakinsu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a wata jihar Arewa yayin da 'yan sanda suka kashe matashi dan shekara 16

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk da cewa, babu wanda zai iya tabbatar da lokacin da abin ya faru, gawarwakin, da aka gano a ranar Alhamis, ya jefa mutanen garin cikin zaman makoki.

Wata majiya a yankin ta fada wa yan jarida cewa dalibin shine da daya kacal da iyayen suka haifa.

Majiyar ta ce:

"Makwabta ne suka gano gawar mutumin da matarsa bayan jin mummunan wari daga dakin. Babu shakka dansu daya kacal da suka haifa ne ya kashe su."

Martanin yan sandan jihar

Kakakin yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce an fara farautar wanda ake zargin.

Ikenga ya bayyana lamarin a matsayin rashin imanin dan adam ga dan adam, ya kara da cewa an gano alamun sara da adda a jikinsu.

Ya ce:

"Kwamishinan yan sanda, CP Echeng Echeng, ya bayyana gano gawarwakin da suka fara lalacewa a wani gida a Nnewi a ranar 22/9/2022 misalin 5.20 na yamma da raunin adda, a matsayin zaluncin dan adam da dan adam.

Kara karanta wannan

Alkawarin Aure: An Fara Gabatar da Shaidu Kan Hadiza Gabon a Kotun Shari'ar Musulunci

"Ya bada umurnin fara farautar wanda ake zargin nan take. Ya kuma ce a tura binciken zuwa sashin binciken manyan laifuka.
"An kuma dauke gawarwakin an kai dakin ajiyar gawa a asibiti."

Dalibin jami'a ya kashe iyayensa da sauran mutanen gidansu, ya ce sun cancanta su mutu

A wani rahoton, Lawrence Simon Warunge, wani matashi mai shekaru 22 da ke karatu a Jami'a, ya amsa laifin kashe iyayensa da sauran wasu mutane uku a Karura da ke yankin Kiambu a kasar Kenya.

Jami'an 'yan sandan kasar Kenya sun sanar da cewa sun kama matashin a ranar Juma'a, 8 ga watan Janairu, bayan shafe kwanaki uku ana nemansa, kamar yadda LIB ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164