Dalibin jami'a ya kashe iyayensa da sauran mutanen gidansu, ya ce sun cancanta su mutu

Dalibin jami'a ya kashe iyayensa da sauran mutanen gidansu, ya ce sun cancanta su mutu

- Wani matashi mai suna Lawrence Simon Warunge ya shiga hannun jami'an tsaro bisa zarginsa da hallaka iyayensa

- Duk da Lawrence ya amsa cewa shine ya kashe iyayensa da sauran mutanen gidansu, jami'an 'yan sanda sun nuna shakku

- A cewar Lawrence, ya samu karfin gwuiwar kashe iyayensa ne bayan kallon wani fim din Turawa

Lawrence Simon Warunge, wani matashi mai shekaru 22 da ke karatu a Jami'a, ya amsa laifin kashe iyayensa da sauran wasu mutane uku a Karura da ke yankin Kiambu a kasar Kenya.

Jami'an 'yan sandan kasar Kenya sun sanar da cewa sun kama matashin a ranar Juma'a, 8 ga watan Janairu, bayan shafe kwanaki uku ana nemansa, kamar yadda LindaIkejisblog ta wallafa.

'Yan sanda sun bayyana cewa Lawrence ya matsa layar zana ranar Talata bayan mutuwar iyayensa, 'yan uwansa guda biyu, da ma'aikaci guda daya wadanda aka yi wa kisan gilla a gidansu da ke mazabar Kiamba.

KARANTA: Fasto Yuana: Shekau yana cikin halin rashin lafiya mai tsanani, yana neman addu'ar Kiristoci da Musulman Nigeria

Bayan kama shi, Lawrence ya amsa cea shine ya hallaka iyayensa da sauran mutanen gidansu tare da jagorantar 'yan sanda zuwa wani wuri a yankin Mai Mahiu inda ya boye kayan da ya yi amfani da domin aikata laifin a cikin wata masai.

Dalibin jami'a ya kashe iyayensa da sauran mutanen gidansu, ya ce sun cancanta su mutu
Dalibin jami'a ya kashe iyayensa da sauran mutanen gidansu, ya ce sun cancanta su mutu @Lindaikeji
Asali: Twitter

Kazalika, ya dauki jami'an 'yan sanda zuwa wani fili da ya yi ikirarin cewa ya kone wasu sauran shaidun.

Duk da Lawrence ya yi ikirarin cewa shi kadai ya aikata kisan, jami'an 'yan sanda sun nuna shakku tare da bayyana cewa zasu kara zurfafa bincike.

KARANTA: Shekau ya saki faifan sako na farko a cikin 2021, ya gargadi Sheikh Ahmad Gumi

Da ya ke amsa tambayoyin jami'an 'yan sanda, Lawrence ya ce iyayensa sun cancanta su mutu saboda sun kasance mugayen mutane marasa tausayi tar da bayyana cewa ya samu karfin gwuiwar kashesu bayan kallom wani fim din Turawa.

A cewar Lawrence, ya yi amfani da wuka wajen hallaka mutanen sannan ya hau achaba, a daren, ya gudu zuwa gidan da budurwarsa ke zaune a Mai Mahiu.

Jami'an 'yan sanda sun bayyana cewa budurwar Lawrence ta shiga hannu amma har yanzu ana neman dan achanar da ya dauko shi daga Kiambu zuwa Mai Mahiu.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa jarumar Kannywood, Rahama sadau, na fuskantar sabuwar caccaka daga masoyanta Musulumai bayan ta sake sakin wani hotonta a dandalin sada zumunta.

Mabiyan jarumar a shafinta na Tuwita sun mayar mata da martani kan hoton da ta ɗauka da jarumar masana'antar Bollywood, Shabnam Surayyo.

Sai dai jarumar ta dawo shafinta na Tuwita ta wallafa wata magana da Priyanka Chopra ta taba yi akan jajiracewa yayin fuskantar suka da tsangwama.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel