Ku Taimaka Ku Yafe Mana Basussukan Da Ake Binmu: Shugaba Buhari Ya Roki Shugabannin Duniya

Ku Taimaka Ku Yafe Mana Basussukan Da Ake Binmu: Shugaba Buhari Ya Roki Shugabannin Duniya

  • Shugaba Buhari ya bukaci shugabannin kasashen duniya su taimaka wajen yafewa Najeriya bashi
  • A jawabin da ya gabatar a majalisar dinkin duniya, shugaban Buhari kasashe da dama na fuskantar kalubale
  • A ranar Litinin, ofishin manajin basussukan Najeriya ya bayyana adadin bashin da ake bin Najeriya ya tashi

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira da shugabannin kasashen duniya su yafewa Najeriya da kasashe masu tasowa basussukan da suke binsu saboda halin matsin tattalin arzikin da suke ciki.

A jawabin da yayi a taron gangamin majalisar dinkin duniya ranar Laraba, Buhari yace kasashe masu tasowa na fuskantar kalubale da dama, cike har da rashin iya bisa basussuka.

Ya bukaci shugabannin duniya su taimaka su sanya baki.

Kara karanta wannan

UNGA77: Shugaba Buhari Yayi Bankwana da Shugabannin Kasashen Duniya

Buhari
Ku Taimaka Ku Yafe Mana Basussukan Da Ake Binmu: Shugaba Buhari Ya Roki Shugabannin Duniya Hoto: Presidency
Asali: UGC

Wani sashen jawabin yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Najeriya na rokon takwarorinmu na duniya su taimaka mana. Lallai kalubalen da kasashe maso tasowa ke fuskanta yasa biyan basussuka zai musu wuya."
"Hakazalika muna kira ga saukake basussukan ta hanyar tsawaita lokuta biya ga kasashe masu fuskantar matsalar kudi da kuma yafiya gaba daya ga kasashen da nasu matsalar tayi tsanani."

Asali: Legit.ng

Online view pixel