Ana Zargin Jami’an ’Yan Sanda da Kashe Mai Sana’ar Hannu Tare da Raunata Mutum Biyu a Jos

Ana Zargin Jami’an ’Yan Sanda da Kashe Mai Sana’ar Hannu Tare da Raunata Mutum Biyu a Jos

  • 'Yan sanda a jihar Filato sun hallaka wani matashi da ke sana'ar hannu a wani rikici da ya barke a kasuwa
  • Mahaifin yaron ya ce sam ba zai amince ba, dole hukumar tsaro ta shiga don gano dalilin kashe dansa
  • Ana yawan samun rikici tsakanin 'yan sanda da fararen hula a Najeriya, lamarin da ke jawo cece-kuce

Jos, Filato Mazauna New Market a karamar hukumar Jos ta Arewa sun zargi 'yan sandan yankin C da aikata zalunci, sun hallaka hallaka wani matashi mai shekaru 16, usman Bala tare da jikkata wasu mutum.

A bisa ga jawaban mutanen wurin, lamarin ya farune tsakanin karfe bakwai zuwa takwas na daren ranan Laraba lokacin da kowa yake hada hadarsa ta yau da kullum.

Kara karanta wannan

Fashin Motar Dakko Kudi: A Yafe Min, Wannan Na Ne Farko, Korarren Jami'in DSS Ya Roki Alfarma

Suna zargin dan sandan ya bude wuta ne akan jama'a da ke harkokinsu na yau da kullum, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

'Yan sanda sun hallaka matashi a Jos
Ana Zargin Jami’an ’Yan Sanda da Kashe Mai Sana’ar Hannu Tare da Raunata Mutum Biyu a Jos | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Naziru Isah Nasale, da ya shaida faruwar lamarin ya fada ma jaridar cewa, lamarin ya faru ne yayin da 'yan sandan suka dira yankin kamar yadda suka saba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"'Yan sandan sukan zo ne daga yankin C domin su yada zango a magamar New Market. Amma kwanaki biyar da suka gabata, matasa na korafin yadda suke zuwa suna kwace keke napep dinsu a yankin.
"To da suka zo jiya, sun kwace wani keke napep, daga nan ne matasan suka fara yi musu ihu, da suke kokarin hana tafiya da keke napep din, 'yan sanda sun bude wuta kan mutane. Sun harbi wani a ciki, wasu mutum biyu kuma a kafa."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kai sabon hari Abuja, mutanen kauye sun nutse garin tserewa

Martanin mahaifin matashin

Mahaifin mamacin, Muhammad Bala ya bayyana yadda ji labarin mutuwar dansa, inda yace bai ji dadi ba kana ya kira hukumar 'yan sanda ta hukunta wadanda suka kashe dansa, Premium Times ta ruwaito.

"Yayin da na isa wurin, an ce min 'yan sanda sun kashe dana. Babu wani jami'in tsaron da yazo gidana domin tattauna wannan lamarin.
"Ba zan iya jure wannan zaluncin ba. Ya kamata kwamishinan 'yan sanda ya shigo lamarin domin gano dalilin yin wannan kisa. Da na bai da wani laifi.
"Aikin hada takalma da jaka yake, ya fita zuwa wani shagon da ke gefe ne domin sayen gam domin hada jaka."

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce 'yan sanda basu je wurin kwace keke napep ba.

Sojojin Najeriya Sun Sheke ’Yan Ta’addan Boko Haram/ISWAP 36, Sun Ceto Mutane 130 a Arewa Maso Gabas

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Wani Kazamin Hari Jihar Neja, Sun Halaka Rayukan Bayin Allah

A wani labarin, hedkwatar tsaro ta Najeriya ya ce dakarun tawagar Operation Hadin Kai ta yi nasarar kawar da 'yan ta'adda sama da 36 a ayyuka daban-daban ta sama a yankin Arewa maso Gabas cikin makwanni biyu.

Daraktan yada labarai na ayyukan soji, Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan a jawabin nasarorin da jami'an tsaro ke samu a yau Alhamis 22 ga watan Satumba a Abuja.

Danmadami ya kuma bayyana cewa, an hallaka kasurguman shugabannin 'yan ta'ddan ISWAP da Boko Haram; Abuja Asiya da Abu Ubaida a aikin, rahoton masanin harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.