Kin yi Sa'ar Mahaifi: Budurwa ta Dauka Bidiyon Mahaifinta Yana Aikin Birkila a Ginin Gidanta
- Wata kyakyawar budurwa ta yi bidiyon mahaifinta yana aikin birkila a filin da take ginawa don ta adana kudinta
- Kamar yadda tace, da kan shi yace zai yi aikin kyauta saboda baya don ta kashe kudi wurin biyan masu kwadago
- Jama’a da yawa da suka kalla bidiyon sun yi martani daban-daban inda wasu suka ce tayi sa’a da samun irin wannan mahaifin
Wata kyakyawar budurwa ta bayyana bidiyon mahaifinta yana aiki matashin birkila yana hada kasa a filin da take ginawa.
Budurwar ta bayyana cewa, mahaifinta ya yanke hukuncin yin aikin ne saboda ta adana kudadenta kada ta kashe tana biyan masu aiki.
Kamar yadda budurwar tace:
“Ya ce da ni kada in bata kudina. Zai iya min a matsayina na diyarsa.”
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kalla bidiyon a kasa:
Jama’a sun yi martani
A yayin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya tara sama da tsokaci 1500 tare da jinjina sama da 7000.
Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin martanin jama’a.
Montreal 2 yace:
"Bambi, na kasa rike hawayena, ina ma mahaifina a raye yake shima, na san cewa zai iya yi min hakan. Na mutunta mahaifinki ta yadda ya samu tsawon kwana har ya ga cigabanki."
SimaGray02 yace:
"Kina da sa'a... Ni ban san ya soyayyar uba take ba kuma duk da yana raye, amma zan tabbatar da cewa yarana sun samu irin mahaifinki."
Danny signal yace:
"A gaskiya wannan abun ya taba zuciyata, wanne irin mahaifin kirki ne wannan."
jamiecurtis56 yace:
"Mahaifin kirki kuma mai kula, Allah ya kara tsawon rai."
Da Digirina na Tafi Libya Aikin Goge-goge: Budurwa 'Yar Najeriya da ake Biya N100,000 Albashi
A wani labari na daban, wata budurwa 'yar Najeriya dake gangariyar turanci a yanar gizo ta koka kan yadda masu digiri ke barin Najeriya kuma suke kananan ayyuka a Libya.
A bidiyon budurwar, tace tana da digiri kuma tana bukatar kudi don yin rayuwa mai kyau. Ta sanar da yacca ake biyanta N25,000 a wata lokacin da take koyarwa a Najeriya.
Budurwar wacce ta lankwasa harshe zuwa ingantaccen turanci domin tabbatar da cewa digiri gareta, ta sanar da cewa tana koyar da ajujuwa shida reras.
Asali: Legit.ng