Neja: An Nemi Wata Mata An Rasa Bayan Saurayinta Ya Kai Mata Ziyara

Neja: An Nemi Wata Mata An Rasa Bayan Saurayinta Ya Kai Mata Ziyara

  • An nemi wata mata an rasa a yankin ƙaramar hukumar Suleja, jihar Neja daga zuwa yi wa saurayinta rakiya tashar mota
  • Makota da kawayen budurwar mai suna, Chiamaka Gregory, sun ce wani saurayinta tun daga Kaduna ya kawo mata ziyara
  • Wata makociya tace sun sanar da yan sanda kasancewar lambar wayarta ba ta shiga, mutane sun fara yaɗa jita-jita

Niger - A ranar Lahadi data gabata, Ƙawaye da makota sun bayyana ɓatan wata mata mai suna, Chiamaka Gregory, a yankin Dwakoro, ƙaramar hukumar Suleja a jihar Neja.

Daily Trust ta tattaro cewa kafin ɓatan Chiamaka, ta sanar da ƙawayenta cewa zata raka saurayinta mai suna Chuks zuwa tashar Mota, wada ya kai mata ziyara tun daga Kaduna ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Wani Kazamin Hari Jihar Neja, Sun Halaka Rayukan Bayin Allah

Taswirar jihar Neja.
Neja: An Nemi Wata Mata An Rasa Bayan Saurayinta Ya Kai Mata Ziyara Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wata maƙociyar matar da ta ɓata, Madam Ruth Innocent, tace, "Bamu sake jin ɗuriyar Chiamaka ba tun lokacin da ta tafi raka saurayinta tashar motar Suleja ranar Lahadi da safe."

"Lambobin wayarta sam ba su shiga, mun sanar da 'yan sanda halin da ake ciki."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka zalika, wani mazaunin yankin, Segun Oguntade, ya shaida wa manema labarai cewa sun yi bincike har sun gaji amma ba su ganta ba.

"Mun nemeta mun bincika ta ko ina, gaskiya mun tsorata saboda kafin yanzu bata taɓa ɓace wa aka rasa inda ta je ba."
Wasu mutane har sun fara raɗe-raɗin cewa mai yuwuwa ta shiga hannun ɓata gari, an yi asirin kuɗi da ita."

Duk wani yunkuri da muka yi na jin ta bakin jami'an hukumar yan sanda dake aiki a yankin da lamarin ya auki bai kai ga nasara ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Kotu Ta Ɗauki Matakin Farko Kan Shari'ar Sojojin da Suka Kashe Sheikh Aisami a Yobe

Meyasa Ɗan China ya kashe budurwarsa a Kano?

A wani labarin kuma Ɗan China Ya Faɗi Babban Dalilin da Yasa Ya Kashe Budurwarsa Ummita a Kano

Geng Quangrong, ɗan asalin ƙasar China mazaunin Kano da ya kashe wata budurwa ya magantu kan dalilin aikata kisan.

A ranar Jumu'a, Deng, wanda bayanai suka nuna suna soyayya da Mamaciyar, ya kutsa har gida ya daɓa mata wuƙa har lahira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel