Yaro Dan Tsugugi Ya Jawo Magana, Ya Sa Mahaifiyarsa Kunci Yayin da Ya Zubar da Manjan N4K

Yaro Dan Tsugugi Ya Jawo Magana, Ya Sa Mahaifiyarsa Kunci Yayin da Ya Zubar da Manjan N4K

  • Wata uwa 'yar Najeriya ta shiga jimami yayin da danta ya zubar da manja kana ya damalmale a ciki yana wasa
  • A wani bidiyon da aka yada a TikTok, an ga lokacin da yaron ke wasa a cikin manja, inda ya ba mahaifiyarsa aikin wanki da tsaftace gida
  • 'Yan TikTok sun magantu, sun ce wannan ba sabon abu bane ganin yadda hali yara yake musamman sadda suka fara tafiya

An ga wani yaron da ya damalmale jikinsa da manja a wani bidiyon da jama'ar intanet suka shiga mamakin gani.

A bidiyon da Mmasi Ivan ya yada a TikTok, an ga yaron yayin da yake wasa da manja a kasan daben cikin gida.

Kamar dai wanda ya samu ruwa da soso da sabulu, yaron ya zauna dabas tana wanke jikinsa da manjan tas.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

Yaro ya wanke jikinsa da manjan N4,000
Yaro dan tsugugi ya jawo magana, ya sa mahaifiyarsa kuka yayin da ya zubar da manjan N4K | Hoto: TikTok/@mmasi_ivan
Asali: UGC

Mahaifiyarsa ta shiga kunci, duk da cewa ta ce ta san tana da wanda zai tsaftace gidan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da ya ga mahaifiyarsa, sai ya yi murmushi ya ci gaba da wasa kamar yadda ya fara.

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan TikTok

Wannan abu dai ya ba 'yan TikTok mamaki, wannan yasa suka yi ta magana a kasan bidiyon.

Wasu sun ce wannan ba sabon abu bane daga yara, wasu kuwa sun ce wannan ba komai bane dace abin dariya kawai.

Ga dai abin da suke cewa:

@NanaSukali242 yace:

"Manja fa? Yaron ba komai yake ba face gyaran jikinsa na yau da kullum."

@Mag Da Lene605 yace:

"Babu abin da zan yi maka, babanka ne zai dawo ya wanke kawai."

@Twinkle Elina yace:

"Mama bamu son irin wannan fa. Ka kyauta sarki Ivan. Muna maka jinjina."

Kara karanta wannan

‘Dan takara Ya Ba Gwamnati Satar Amsar Magance Matsalar ASUU a Kwana 30

@user2781547183671 yace:

"Har wani wasa yake a inda ya tafka laifi....Ina son wannan yaron."

Bayan Mutuwar Mahaifinsu, Wani Ahali a Najeriya Sun Gano an Binne Maciji a Tsakiyar Dakinsa

A wani labarin, hoton wani mataccen maciji ya yadu a kafar Twitter yayin da wasu ahali 'yan Najeriya suka bayyana gano shi a dakin mahaifinsu.

Abin da ya ba jama'a da dama mamaki shine, mahaifin nasu tuni ya mutu, lamarin da ya kai suka fara zargin macijin na da alaka da mutuwar.

A cewar mutumin da ya yada hoton, dama an ba su shawarin su tone daben dakin mahaifin nasu, sai yanzu suka samu damar yin hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel