NDLEA Ta Yi Babban Kamu, Sai da Buhari Ya Kira Janar Buba Marwa ta Wayar Salula

NDLEA Ta Yi Babban Kamu, Sai da Buhari Ya Kira Janar Buba Marwa ta Wayar Salula

  • Nasara bayan nasarar da Janar Buba Marwa (rtd) yake samu a NDLEA ya burge Muhammadu Buhari
  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kira shugaban hukumar NDLEA ta wayar salula daga Amurka
  • Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar da jawabi, yana cewa Buhari yana alfahari da aikin Marwa

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jinjina na musamman ga shugaban hukumar NDLEA ta kasa watau Buba Murwa kan irin kokarin da yake yi.

Kamar yadda jaridar The Cable ta kawo rahoto, Muhammadu Buhari ya kira Buba Marwa ta wayar salula domin yabawa abin kwazon da jami’ansa suke yi.

Yabon da shugaban kasa ya yi wa Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya zo ne bayan jami’an NDLEA sun yi nasarar karbe tulin hodar iblis a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Dan China Ya Yaudari Ummita a Kan Shiga Musulunci inji Babbar Kawar Ummita

Rahotanni sun ce darajar hodar iblis da aka karbe a yankin Ikorodu a Legas ya kai na N194b.

Femi Adesina ya fitar da jawabi

A jawabin da Femi Adesina ya fitar a ranar Litinin, an ji cewa Mai girma shugaban kasa ya kira Janar Marwa yayin da yake halartar taron UN a Amurka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ina mai matukar godewa aikin da ka ke yi wajen magance matsalar miyagun kwayoyi. Ina farin cikin ganin irin nasarorin da ake samu a karkashinka.
Shugaban NDLEA
Janar Buba Marwa da Shugaban kasa Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

“Ka na ta kara nuna ba ayi tumin-dare wajen zabenka da aka yi a matsayin wanda zai jagoranci wannan yaki da masu nema hallaka matasanmu ba.”
“Ka cigaba da namijin kokarin da kake yi.”

- Muhammadu Buhari

Shugaban kasa ya yi murna

Leadership take cewa Mista Adesina yace Muhammadu Buhari ya nuna farin cikinsa ga NDLEA a gaban tawagarsa da ke halartar taron majalisar dinkin Duniya.

Kara karanta wannan

An Jefar da Karar da Abduljabbar Kabara Ya Kai Gwamnati, An Ci Shi Tarar N100, 000

An ji shugaban kasar yana yabawa shugaban na NDLEA a zamansa da abokan rakiyarsa.

“Buba Marwa yana kokari. Tan biyu na hodar iblis, wannan gagarumin aiki ne.”

- Muhammadu Buhari

Rokon gwamnonin Arewa

Kun ji labari Kungiyar Gwamnoni ta ‘North East Governors Forum’ tana so a dage da aikin wutan Mambila Hydroelectricity domin a samu lantarki.

Gwamnonin sun ankarar da Gwamnatin Najeriya cewa yankin na Arewa maso gabas ba zai taba cigaba ba tare da wutar lantarki da zaman lafiya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng